Masu Mukamai a gwamnatin Kano ba su da uzurin kin taimakawa yan Kwankwasiyya – Sanusi Bature

Date:

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yana iya bakin kokarinsa wajen taimakon yan jam’iyya.

“Ni dai a sani na ban taba ganin Gwamnan dake taimakon ‘yan jam’iyyar sa ciki har da ‘yan gwagwarmaya ba kamar Gwamnan Kano H.E. Abba Kabir Yusuf”.

Gwamna ya raba kujerun Makka, ya raba Umrah, ya raba babura, motoci da gidaje kuma yana bada jari da Gwamnatance da kuma ta aljihunsa kai tsaye.

FB IMG 1753738820016
Talla

Sanusi Bature ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook.

Ya ce “Tun da aka kirkiri Jihar Kano babu Gwamnan da ya bada tallafi ga masu rashin lafiya cikin ‘yan jam’iyya, masu ruwa da tsaki da sauran al’ummar gari kamar Gwamna Abba Gida Gida…

Amma fa hannun Gwamna ba zai kai kan kowa ba saboda yawan mutane, kuma akwai hakki akan mu da ya dorawa nauyi na mukamai, ba mu da wani uzuri idan bamu rage masa aiki ba wajen tallafawa na kasa damu ko kuma makusantan mu a wannan harkar.

Magoya bayan Barr Ibrahim Isa (Matawallen Gwagwarwa) sun aikawa Gwamnan Kano Budaddiyar Wasika

Wallahi da yawan mu kuma muna kokari wajen rage nauyin, amma wasu gajen hakuri ne da su, wasu kuma wallahi bama mu san sun bada gudunmawa ba, saboda mutanen da yawa.

Amma ba laifi ba ne idan anci gaba da haskawa jami’an Gwamnati wadanda su ka sha walaha a harkar kuma suke da bukatar taimako.

“Wallahi ko irin su SSAs din nan da kuke gani irin su Salisu Yahaya Hotoro da Muhammad Sani Isah Romi da su Abubakar Muhammad Inuwa dama Salisu Kosawa suna samun abin da za su taikamaki ‘yan uwan su ‘yan gwagwarmaya”  Inji Sanusi Bature

Saboda haka babu wani uzuri ga wadanda su ki taimakon yan jam’iyya musamman wadanda aka yi gwagwarmayar yakin neman zabe a 20219 da 2023 dasu.

Ya kara da cewa “Ni dai kam, kada Allah ya bani abin da ba zan iya taimakawa wani da shi ba, ko mene ne na gidan duniyar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nan gaba kadan za mu bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya – Babban Hafsan tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce...

Wasu yan daba sun ajiye Makamansu a Kano

Gwamnatin Jihar Kano Hadin gwaiwa da Rundunar Yansandan Jihar...

Magoya bayan Barr Ibrahim Isa (Matawallen Gwagwarwa) sun aikawa Gwamnan Kano Budaddiyar Wasika

Daga Isa Ahmad Getso Kira don nemawa Barr. Ibrahim Isa...

Bukatun Nigeria da Tinubu ya mika a taron da ake yi a Japan

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi kiran samar da...