Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rantsar Alhaji Sa’idu Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
Da yake rantsar da sabon shugaban a gidan gwamnati, gwamna Abba Kabir Yusuf ya hore shi da ya zamo mai gaskiya da amana a yayin gudanar da aikinsa.

Yace gwamnati ta bashi wannan mukami ne la’akari da gudummawar da yake bayarwa wajen yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano da ma kasa baki daya.
Ya hore shi da ya zamo mai jajircewa da sadaukar da kai tare da tabbatar da adalci ga kowane bangare.
Magoya bayan NNPP Kwankwansiyya a Bagwai na neman agajin Gwamnan Kano da Dungurawa
Kazalika gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da karin masu bashi shawara na musamman da suka hadar da tsohon shugaban hukumar tallafin karatu ta jiha Alhaji Kabiru Haruna Ketso da Alhaji Sale Musa Sa’ad da kuma Sylvester Kole.
A nasa bangaren, sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jiha, Alhaji Sa’idu Yahaya ya yi alwashin gudanar da aikinsa bisa gaskiya da mana tare da yin aiki bisa tanadin doka domin tabbatar da kyakkyawan zaton da ake dashi a kansa.