NNPP ta yi watsi da sakamakon Zaben Ghari da Tsanyawa a Kano

Date:

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen da aka maimaita na majalisar jiha da aka gudanar a mazabar Ghari/Tsanyawa, tana zargin an tafka magudi tare da haɗin baki tsakanin ‘yan siyasa da jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Yayin da yake zantawa da manema labarai, shugaban jam’iyyar na jiha, Kwamared Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya zargi INEC da “ƙin ba wa masu zaɓe haƙƙinsu” bayan da ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Kwankwaso ya yi tsokaci game da zaben cike gurbi da akai a Kano

NNPP ta bayyana cewa zaɓen ya kamata a gudanar da shi ne a rumfunan zaɓe 10 da kotun daukaka ƙara ta soke sakamakonsu, amma ta yi ikirarin cewa INEC ta soke sakamakon rumfunan sannan ta koma kan tsohon sakamakon da kotu ta riga ta ƙi amincewa da shi.

FB IMG 1753738820016
Talla

“A Ƙaramar Hukumar Ghari, an gudanar da zaɓen cikin lumana a rumfunan zaɓe 10, amma ta hanyar magudi da wasu ‘yan siyasa marasa kishin ƙasa suka yi tare da haɗin gwiwar jami’an INEC, aka ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya yi nasara,” in ji jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kuma soki INEC bisa ayyana sakamakon a babban ofishinta na jihar Kano maimakon cibiyar tattara sakamakon mazabar, tana zargin hakan ya ba da damar tafka magudi.

NNPP ta sha alwashin ci gaba da adawa da abin da ta bayyana a matsayin rashin adalci, son kai da kuma maguɗin zaɓe, tana jaddada cewa jami’an gudanar da zaɓe a rumfunan sun riga sun sanya hannu kan sakamakon da ya kamata a tabbatar da shi.

Sai dai jam’iyyar ta yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cike gurbi na Shanono/Bagwai, inda ɗan takararta ya yi nasara, tana bayyana tsarin a matsayin sahihi. Ta kuma gode wa jami’an tsaro bisa samar da yanayi mai kyau da kuma jinjina wa masu zaɓe saboda fitowarsu da yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Adam A Zango ya sake Aurar Jarumar Kannywood

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, Adam A....

Kwankwaso ya yi tsokaci game da zaben cike gurbi da akai a Kano

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana...

A Hukuma ce INEC ta bayyana sakamakon zabukan cike gurbi da aka yi a kano

Hukumar zabe mai zamanta ta Kasa ta bayyana Dan...

PDP ta yi watsi da zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono dake Kano

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya...