Daga Isa Ahmad Getso
Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Kano ta Sanya dokar takaita zurga-zurga a kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa da kuma Bagwai da shanono, inda za a gudanar da zaben cike gurbi a ranar asabar mai zuwa .
” Dokar za ta Fara aiki daga 12 na daren Ranar juma’a har zuwa karfe 06 na yammacin Ranar Asabar 17 ga watan Augusta, 2025, an haramtawa kowa yawo da makami ko wata alamar jam’iyya a ranar zaben”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya Sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Ya ce Rundunar ta shirya tsaf domin Samar da ingantaccen tsaro a wadancan kananan hukumomin da za a gudanar da zaben .

Sanarwar ta ce Rundunar zata hada Kai da dukkanin hukumomin tsaro dake jihar Kano don tabbatar da an yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Kiyawa ya ce Rundunar ta kuma haramtawa yan KAROTA da yan vigilante da Shiga cikin aikin Samar da tsaro a kananan hukumomin da za a gudanar da zaben .