Daga Umar Ibrahim Usman
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya mika ta’aziyya ga gwamnatin Ghana da iyalan wadanda rasuwar mutane takwas a hatsarin jirgin soja ta shafa a kasar.
A sakon da mai magana da yawunsa ya Sarkin Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa Kadaura24 ya ce Sarkin ya bayyana wannan a matsayin babban rashi ga Ghana, Najeriya, da ma yankin Afirka ta Yamma baki ɗaya.

Ya mika sakon jaje da addu’a ga dangin mamatan da al’ummar Ghana, yana roƙon Allah Ya jikan su da rahama kuma Ya bai wa iyalan da ‘yanuwa haƙuri da juriya.
Gwamnan Kano ya Gabatarwa Majalisar Dokokin Jihar Wasu Manyan Bukatu
Idan dai ba a manta ba cikin mutanen takwas da su ka rasu a hadarin jirgin saman mai saukar ungulu akwai wasu ministoci biyu na tsaro Edward Omane Boamah da ministan muhalli Braham Murtala Muhammed da suka rigamu gidan gaskiya a hadarin na yankin Ashanti a daji da ke kusa da Obuasi.