Daga Isa Ahmad Getso
Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi wasu jerin bukatu daga gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
A sakon da mai magana da yawun shugaban majalisar dokokin jihar Kano Jibril Isma’il Falgore wato Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar ya bayyana cewa cikin bukatar da Gwamna Yusuf ya gabatar ya hadar da gabatar da sunan Saidu Yahaya don a tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar da ke karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa wato (Public Complaints and Anti-Corruption Commission). A cewar Gwamnan Yahaya an gabatar da sunansa ne saboda cancantarsa da daraja da gogewa da yake da su tsawon lokaci a wannan fanni.

A wata bukatar da gwamnan ya gabatar ta hadar da bukatar majalisar ta sahale wa gwamnatin ta Kano kudirin kwarya-kwaryar kasafin kudi na shekarar 2025.
Gwamnan Kano ya raba tallafin kayan sana’o’i ga matasa 1130
Wannan bukata na zuwa ne yayin da gwamnatin Kano ke son gudanar da wasu muhimman ayyukan na samar da ababen more rayuwa a fadin jihar ta Kano, musamman a kwarayar birnin na Kano cikin ayyukan sabunta birnin. Hakazalika a kudirin zai duba batun samar da sabbin ma’aikatu da sassa da wasu cibiyoyi na gwamnati da za su taimaka a habbaka ayyuka na ci gaba cikin gaggawa.

Kwarya-kwaryar kasafin dai ana tsammanin ya kai ₦169,522,463,294.81.
Wannan bukata dai ta samu karbar majalisar dokokin jihar ta Kano inda shugaban majalisar Falgore ya gabatar da bukatar ga kwamitin majalisa mai kula da kasafi wanda zai duba ya kuma amince da bukatar.