Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Gwamnatin jihar Kano karkashin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta amince da korar wasu manyan Hadiman gwamnan guda biyu nan take, bayan Samun su da hannu a takaddamar belin wanda ake zargi da safarar kwayoyi da kuma wasu laifuka na daban.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar ranar Asabar, kamar yadda Sakataren yada labaran ofishin Sakataren gwamnatin Musa Tanko Muhd ya aikowa Kadaura24.

A wani gagarumin mataki da gwamnan ya dauka, ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa, bayan da kwamitin bincike na musamman ya tuhume shi a matsayin wanda ya shirya belin Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ya tabbatar da laifin Abubakar Sharada a cikin takaddamar belin ta hanyar bincike da kwamitin da ya gabatar .
A cewar wata wasika da ya fitar a ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta 2025, sakataren gwamnatin jihar Kano, ya umarci Sharada da ya mika dukkan kadarorin gwamnati dake hannunsa zuwa ofishin SSG, a ranar ko kafin rufe aiki a ranar Litinin, 11 ga Agusta 2025.
A karon farko gwamnatin Abba gida-gida ta yi koyi da ta Ganduje
An kuma gargade shi da kada ya sake bayyna kansa a matsayin jami’in wannan gwamnati mai ci.
Hakazalika, gwamnan ya sauke Tasiu Adamu Al’amin Roba, babban mataimaki na musamman a cabinet office, daga mukaminsa bayan Samun shi da laifin sake yin buhunan hatsi a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada a shekarar 2024.
Tuni dai aka gurfanar da Roba a gaban kotu, kuma yana fuskantar tuhumar sata da hada baki da laifin karkatar da kadarorin jama’a.
Haka kuma an umurci Tasiu Adamu Al’amin Roba da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannun sa da suka hada da ID Card a ranar Litinin ko kuma kafin ranar Litinin 11 ga watan Agusta 2025. Ya kuma yi gargadin kada ya sake bayyana kansa a matsayin ma’aikacin Wannan gwamnatin mai ci.

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar ta wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, mai ba shi shawara na musamman kan magudanun ruwa, wanda kwamitin bincike ya wanke shi daga dukkan zarge-zargen, inda ya tabbatar da cewa ba shi da laifi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tabbatar da adalci da kuma rashin amincewa da cin hanci da rashawa, yana mai gargadin dukkanin jami’an gwamnati da su kasance masu bin ka’ida a ayyukansu.
A cikin wannan sanarwa, ana shawartar jama’a da kada su shiga hannun wasu mukaman siyasa biyu da aka kora a kan duk wani batu da ya shafi gwamnatin jihar Kano, duk wanda ya yi haka, ya yi ne a kan kansa