Tinubu ya yi wa Buhari abun da Buharin ya kasa yi wa kakana- Jikan Shagari

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Nura Muhammad Mahe, jikan tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari, ya yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa yadda ya karrama marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yadda ya tsaya akai komai da shi yayin jana’izar Buhari , inda ya bayyana hakan a matsayin alamar jagoranci na gaskiya da hadin kan kasa.

Sai dai ya yi koka da yadda marigayi shugaban kasa Buhari ya kasa yi wa kakansa Alhaji Shagari irin wannan karramawa a lokacin da ya rasu a shekarar 2018.

A wata sanarwa da ya fitar a Sokoto ranar Laraba, Mahe ya yaba wa Tinubu kan halartar jana’izar Buhari da kuma kafa wani kwamiti mai karfi da zai shirya jana’izar, inda ya ce irin wadannan ayyuka na nuna matukar mutunta tarihin kasar da kuma shugabanninta.

InShot 20250309 102512486
Talla

“Wannan abun da Tinubu ya yiwa Buhari ya bambanta da yadda aka yi wa kakana, Shugaba Shehu Shagari, a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari,” in ji Mahe.

Ya bayyana cewa bayan rasuwar Shagari a shekarar 2018, tsohon shugaban kasa Buhari bai halarci jana’izar ba kuma an yi wani abu na nuna karramawa ga shagari ba duk da cewa yana kasar a lokacin da aka yi rasuwar.

Idan za ku iya tuna clMarigayi Shugaba Shagari ya rasu ne a ranar 28 ga watan Disamba, 2018 kuma an yi jana’izarsa a ranar 29 ga Disamba, 2018.

Sai dai Marigayi Shugaba Buhari ya je Sokoto domin yin ta’aziyyar marigayin tare da sanya hannu kan takardar wadanda suka je ta’aziyyar.

Yadda mu ka yi da Buhari kwana daya kafin rasuwarsa – Mamman Daura

Da yake nuna takaicin rashin kulawa da kakansa, Mahe ya ce, maimakon Buhari ya halarci jana’izar a lokacin, sai ya aika “tawaga karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, domin su wakilci gwamnati.

“Wannan abun bai yi wa iyalan Shagari da ‘yan Najeriya Dadi ba, domin da yawa sun yi tsammanin Buhari zai karrama shagari kamar yadda Tinubu ya yi masa, a matsayin shagari na tsohon shugaban Nigeria Mai cikakken iko na farko,” in ji Mahe.

Ya bayyana rashin kulawar da Buhari ya yi wa Shagari da cewa ana ganin tana nasaba da banbancin siyasa, Amma duk da haka Muna ganin ya kamata Buhari ya karrama kakana saboda tsohon shugaban Kasa ne.”

Ko da aka tuntubi Garba Shehu Mai magana da yawun Buhari akan Maganar , yaki cewa komai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...

Zargin kwace gona: Majalisar Dokokin Kano zata binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada (ALGON)

    Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha alwashin gudanar da...

Yanzu-yanzu: Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fice daga...

Gwamnatin Jihar Kano ta fara bincike kan mutuwar wasu ɗaliban makarantar Sakandare biyu

  Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Makoda, ya...