FUDMA ta Sanya Sunan Farfesa Gwarzo a kan Babban Titin Jami’ar

Date:

An sanya sunan Farfesa Gwarzo a kan babban titin Jami’ar FUDMA
Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsin-Ma dake jihar Katsina, ta karrama shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University Niger (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, inda ta sanyawa babban titin shiga Jami’ar sunansa.
An yi bikin kaddamar da titin ne a jiya Asabar a yayin bikin yaye daliban Jami’ar .
A lokacin da yake bayyana makasudin sanya sunan Farfesa Gwarzo a babban titin Jami’ar, Alhaji Uba Ahmad Nana, ‘Pro- Chancellor’ kuma shugaban Majalisar gudanarwa ta Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsin-Ma, ya ce sun sanyawa titin sunan Farfesa Gwarzo ne bisa yadda yake tallafawa Jami’ar da ma al’umma baki daya.
“wannan titin an sanya masa sunanka ne bisa ayyukan rashin son kai da kake yi wa al’umma, da kuma karamcinka da taimakon jama’a, ba kawai ga FUDMA ba, harma da sauran al’umma baki daya. Allah ta’ala cikin Rahamarsa ya saka maka da alherinsa mai yawa. Kana matukar tallafawa Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsin-Ma. Kuma mun tattaunawa a kan ka a lokuta daban-daban, Shugaban Jam’iar ya yi min bayani sosai a kanka da ayyukan da kake yi”, inji shi. 
Alhaji Nana har wala yau ya ci gaba da cewa, ayyuka da tallafin da Farfesa Gwarzo yake yi wa FUDMA ba batu ne na a rubuta takardar godiya ba; “mun ga yakamata mu ziyarceka a inda kake domin mu mika sakon jindadinmu da godiyarmu bisa abin da kake yi mana a nan, amma hakan bai yiwuwa ba saboda a lokacin ba ka kasa. Ba ma kawai a Dutsin-Ma ba, a ko’ina.
Muna matukar godiya sosai, za mu ci gaba da mika godiyarmu. Bisa wannan, a madadin Majalisar gudanarwa, membobin majalisar, ma’aikata da dalibai na Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsin-Ma, zan mika wannan titin da aka sanyawa sunanka , yanzu za ka kaddamar da shi bisa tallafi da hidima na rashin son kai da kake yi wa al’umma. Za mu ci gaba da kasancewa cikin godiya. Muna rokon Allah ya yi wa rayuwarka albarka”, ya jaddada.
Ya kara da cewa; “Zan baka (abin magana) domin ka kaddamar da wannan aiki da aka karramaka da shi bisa ayyukan da kake yi wa al’umma”.
A na shi bayanin, shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University Niger (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana jindadinsa da farin cikinsa bisa wannan karramawar da aka yi masa na sanya sunansa a babban titin shiga Jami’ar ta FUDMA, inda ya ce; “nagode sosai bisa wannan karramawar. Ina godiya sosai. Allah ya yi muku albarka. Zan ci gaba da kulla alaka da Jami’ar Dutsin-Ma. Dukkannin tallafina da kwarewata kan inganta jami’a a matakin da duniya take a kai, da kuma bayar da ilimi ba tare da iyaka ba, zan raba shi da Jami’ar Dutsin-Ma, nagode”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...