Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa
A makon da mu ka yi bankwana da shi ne kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya cika kwanaki 100 yana jagorantar ma’aikatar yada labarai ta jiha da kuma kasancewarsa mai magana da yawun gwamnatin jihar Kano.
Kadaura24 za ta yi duk dangane da aiyukan da kwamishina Waiya ya gudanar cikin wadancan kwanaki 100 da su ka gabata idan ya so mai karatu sai ya lissafin ya gani riba aka samu ko faduwa a tsahon wadancan kwanaki.
Mai karatu ya sani wannan rubutun ba daukar nauyinsa aka yi ba, kawai Kadaura24 ta yi shi ne domin fito da wasu abubuwa da ya kamata al’umma su sami.

A ranar 7 ga watan Janairu, 2025, Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya a matsayin kwamishina kuma aka tura domin jagorantar ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida.
Tun daga Wannan lokaci Waiya ya kama aiki tare da fito da sabbin tsare-tsare wadanda a karan kansa ya aminta za su taimaka wajen inganta aikin yada labarai a jihar Kano.
Inganta aiki ga ma’aikata:
Tun farkon zuwansa Kwamishina Waiya ya yi alkawarin rika baiwa jami’an yada labarai horo tare da shirya musu bitoci domin su rika aikinsu na yada labarai daidai da zamani. Hakan ta sa ya shirya musu wata bita ta musamman inganta aka ba su horo kan yadda za su rika amfani da kafofin sadarwa na zamani don inganta aikinsu da kuma saukaka musu.
Bayan ga wannan Waiya ya samar da wani asusu na taimakekeniya wanda zai baiwa ma’aikatan damar tara kudi a cikin dan abin da suke samu domin taimakon kansu da kansu, kuma bayar kaddamar da asusun ya ba su gudunmawa domin kara musu kwarin gwiwa.
Hajjin Bana: An sanya ranar da Alhazan Kano za su fara tashi zuwa Saudiyya
Haka dai take ta fito da tsare-tsare wadanda za su samar da walwala ga ma’aikatan don su ji dadin gudanar da aiyukansu yadda ya dace.
Hada Kan Yan Jarida ake aiki a Kano:
A kokarinsa na inganta dangantakar dake tsakanin gwamnatin jihar Kano da yan jaridu, kwamishinan yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya himmatu domin ganin ya hada kan yan jaridun don su amfana da gwamnati yadda ya dace kuma ita ma gwamnatin ta amfana da su yadda ya kamata.
Kafin zuwansa yan jaridun dake aiki yada labarai ta Internet kansu a rabe yake,amma yanzu Waiya ya yi nasara sasanta Wannan Rikici kuma sun shiga cikin uwar kungiyar yan jaridu ta kasa wato NUJ.
Lokaci zuwa lokaci ya kan gana da tsofaffin yan jaridu domin ganin su na ba da shawarwari musamman ga ita kungiyar NUJ don ganin an tsaftace aikin jarida a Kano. Hakan ta sa lokacin Azumi ya shirya wani taro bude baki da yan jaridu wanda hakan shi ne irinsa na farko kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an sami fahintar juna tsakinsu.
Haka zalika, ya yi kokari wajen ganin an masu gabatar da shirye-shiryen siyasa a gidajen Radio a Kano suma sun samar da kungiya wadda hakan zai taimake su matuka, kuma tuni suka fara ganin ribar hakan.
Magance Kalaman batanci a gidajen Radio
Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya a wannan bangaren ma bai zauna ba, domin ganin an kawar da siyasar cin zarafin al’umma da ake zargin sojojin baka na yi a Shirye-Shiryen Siyasa da ake gudanarwa a Kano.
Ma’aikatar yada labarai ta Kano ta shirya bitar yini 2 ga sojojin baka
Bayan tattaunawa da masu magana akan harkokin siyasar a radio, ya umarcesu da su fito da samar da kungiyar domin ganin an hadesu karkashin inuwa guda, wanda hakan ya sa suka farfado da kungiyar Gauta Club.
Ya kan zama da su akai-akai domin ganin ya cimma manufofinsa na magance Kalaman batanci akan kowa a Kano ba tare da la’akari da banbancin jam’iyya ba. A makon da muka yi bankwana da shi ne Kwamared Waiya ya shiryawa sojojin baka bita domin fadakar da su illolin cin mutuncin mutane a mahanga ta addinin musulunci da kuma rayuwa.
A yayin bitar Kwamishinan ya bayyana cewa yana wannan kokari ne ba wai don ya hana yan adawa yiwa gwamnati adawa ba, kawai yana hakan ne domin ganin ana yin siyasar cikin mutunci da girmamawa sabanin yadda ake yi a baya.
Wadannan su ne wasu daga cikin nasarorin da mu ke ganin Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya samu cikin kwanaki 100, duk da cewa ba wai iya kacinsu kenanba, amma da wadannan su ne muke ganin na kan gaba cikin nasarorin.
Hakan kuma baya nuna cewa ba wasu kura-kurai da kwamishinan yayi tun tsahon wadancan kwanaki, kasancewarsa dan Adam dole a sami kura-kurai wadanda mu muka sani da wadanda mu ba mu sani ba.
Sai dai dama so ake daidan kowanne mutum ta rinjayi kura-kuranshi.