Zaharadeen Saleh.
Kungiyar kwallon kafa ta Mailantarki care dake birnin tarayyar Abuja, ta musanta zargin da jami’in tsare tsare na kungiyar Flying eagles ta kasa Abubakar Dan Fulani yayi akan shugaban kungiyar Mailantarki, Alhaji Khamisu Ahmed Mailantarki akan yana da hannu wajen hana tafiya da dan wasan kungiyar Haruna Aliyu, gasar kasashen nahiyar afrika ta Yan kasa da shekaru ashirin wadda zai gudan a kasar masar.
Daraktan yada labarai na kungiyar Adamu Usman Ahmed, ne ya musanta zargin a wata sanarwa daya fitar mai dauke da sa hannu sa, a inda yace wannan labari da Abubakar Dan Fulani, bashi da tushe ballanta na makama.
Sanarwar ta Kara da cewa mun samu labarin jami’in Flying Eagles Abubakar Dan Fulani yayi hira a gidan Rediyon Amana dake jihar Gombe, yana yiwa Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki kazafin shine ya hana Haruna Aliyu ya shiga cikin tawagar kungiyar kwallon kafa ta flying eagles ta Nigeria bisa dalilin korafi daya mika wa hukumar kwallon kafa ta kasa, a cewar Abubakar Dan Fulani.

Adamu Usman yace Dan Fulani yana so ne yayi amfani da damar sa ne ya bata sunan shugaban kungiyar kwallon kafa ta Mailantarki saboda dukkan su sun fito ne daga jihar Gombe, tare da kalamai masu dauke da bacel masu kama dana siyasa duba da cewa Hon Mailantarki jigo ne a jamiyyar adawa a jahar ta Gombe.
Haruna Aliyu wadda kawo yanzu dan wasan Doma United ne amma tunin ya sanya hannu a hukumance a wata takarda wa kungiyar ta Mailantarki hakan ya bashi damar zama dan wasan kungiyar da zarar karshen kakar gasar kwararru aji na biyu wato NNL tazo karshe nan da yan watanni, amma daga bisani dan wasan ya sake saka hannu a wata kungiyar wadda hakan ya saba doka.
Ma’aikatar yada labarai ta Kano ta shirya bitar yini 2 ga sojojin baka
Duba da irin yadda dan wasan Haruna Aliyu ya jefa kansa a rikita-rikita tare da biye wa gurguwar shawara sakamakon halin da Abubakar (Yellow) ya tsunduma shi ne ya sake kulla yarjejeniya da wata kungiyar, bayan tunda farko yana da yarjejeniya daya kulla da kungiyar Mailantarki kamar yadda daya daga cikin jami’in kungiyar Mailantarki Auwal Kawuwa ya tabbatar da hakan a hirar sa na mayar da martani tare da gidan Rediyon Amana dage Gombe, hakan ne yasa aka cire sunan dan wasan wadda hukumar kwallon kafa ta kasa tayi, duba da ita hukumar tana sane da yarje jeniya da dan wasan ya kulla da Mailantarki daga farko, sannan daga bisani ya kuma sanya hannu a wata kungiya ta daban a baya-baya nan yayin da suke karbar horo a sansani atisaye din kungiyar Flying eagles ta domin tunkarar gasar nahiyar afrika ta yan kasa da shekaru 20.
Hon. Khamisu Ahmed shine mai kungiyar Mailantarki Kuma mutum ne mai son cigaban Yan wasan jihar Gombe, da kuma Arewacin Nigeria da baki daya. Wannan shi ya sanya mai da hankalin yayi kokari ya samarwa dan wasan gurbin gwaji daga bisani ya nuna bajinta ya samu damar shiga tawagar a shekarar 2023 wadda daganan ya samu damar zuwa gasar wasannin Africa ba tare da wata tasgaroba, lokacin ba’a dauki Abubakar yellow a kungiyar ta kasa ba.
Dan wasan Haruna Aliyu ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Mailantarki care a kakar wasa ta shekara 2024 zuwa 2025 a gasar ajin kwararru ta kasa, yace har yanzu Haruna Dan wasan kungiyar Mailantarki har sai an kammala kakar wasa ta bana amma Kuma ya Kara Sanya hannu a wata kungiyar.
A karshe kungiyar kwallon kafa ta Mailantarki Care FC tayi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da suyi watse da labaran yarfe da Abubakar Dan Fulani ( Yellow) yake yadawa akan shugaban kungiyar Mailantarki Care FC Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki.
Yan wasan kwallo da dama ne daga jahar Gombe hada da sauran jahohin arewa da Nigeria baki daya samu gagarumar dama karkashin daukar nauyin shugabar guniyar Mailantarki Care FC, inda wasu sukayi nasarar samu kulob a nahiyar turai wasu Kuma sun dawo suna cigaba da karbar horo na musamman kafun su koma.
A dalilin haka al’umma ya kamata su jinjina masa bisa abun a yaba da Mailantarki yakeyi don kawo ciki da gaggarumar basara harkan wasan kwallon kafa a Nigeria, kamar yadda Malam Farouk Yarma yakeyi na karrama masu kokarin ciyar da harkar wasanni gaba a karkashin kamfanin sa ta ‘Prudential Sports Limited’.