Gwamnonin jihohin Nijeriya sun fara wani yunkuri na dakatar da shirin tura wa kananan hukumomin kasar kason kudaden su kai tsaye.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tsaiko wajen aiwatar da hukuncin kotun koli kan ‘yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi.

Wasu daga cikin gwamnonin da suka gana da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Talatar makon jiya, sun yi watsi da matakin babban bankin Nijeriya CBN na tura kudin kai tsaye, inda suka bayyana cewa ana bin kananan hukumomin tulin bashi.
Yanzu-yanzu: EFCC ta bayyana dalilan da su ka sa ta kama Jarumar Tiktok Murja Kunya
Majiyoyin jaridar Punch a fadar shugaban kasa sun ce, gwamnonin sun nemi shugaban da ya sake duba kan lamarin.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a shekarar da ta gabata ne Kotun kolin Nigeria ta tabbatar da yankin cin gashin kan kananan hukumomi a Nigeria.