Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi da tsohon Kwamishinan sa ido da tantance ayyukan gwamnatin Kano Muhammad Diggol sun gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin a Abuja.
Ganawar wanda ta haɗa sauran masu ruwa da tsaki, ta mayar da hankali ne kan samar da ci gaba a Jihar Kano da kuma ciyar da ƙasa gaba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau ya wallafa hotunan ganawar da aka yi tare da bayyana muhimmancin haɗin gwiwa wajen samun ci gaba mai ɗorewa.
“Ci gaban jiharmu da ƙasa a kodayaushe yana kan gaba a ajandarmu, za mu ci gaba da haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki domin ciyar da jiharmu da ƙasa gaba,” in ji shi.
Kadaura24 a ruwaito cewa taron na daga cikin ƙoƙarin da shugabannin siyasa ke yi na yin cuɗanya da manyan mutane a ci gaban Jihar Kano da kuma yin aiki da manufa guda domin samun ci gaba