Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

Date:

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun daukaka kara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke ranar 10 ga watan Janairu wanda ya tabbatar da matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na soke dokar majalisar masarautun ta shekarar 2019, har sai an yanke hukuncin daukaka kara a kotun koli.

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Kano ta yi watsi da umarnin da Mai Shari’a Abubakar Liman na babbar kotun tarayya da ke Kano ya bayar a ranar 20 ga watan Yuni, inda ta soke matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka bisa dokar masarautar Kano ta 2024, ciki har da nadin Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16.

An yi karar gwamnatin jihar Kano, da kakakin majalisar dokokin kasar, da babban sufeton ‘yan sanda, da hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, da jami’an tsaron civic defence, da sauran hukumomin tsaro.

InShot 20250309 102403344
Talla

Aminu Baba Dan (Sarkin Dawaki Babba), a karar da ya shigar a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, ya nemi umarnin hana wadanda ake kara aiwatar da hukuncin kotun daukaka kara a yayin da ake ci gaba da daukaka kara a kotun koli.

Dalilin da ya sa aka shigar da karar shi ne tun da farko wanda ya shigar da karar ya shigar da karar ne a Kano don neman kare masa hakkinsa,wanda aka ce kotun da ke shari’ar ba ta da hurumin saurare karar, don haka akwai bukatar a hana wadanda ake kara aiwatar da hukuncin.

A cikin hukuncin da aka yanke, tawagar alkalan guda uku dake karkashin jagorancin Abang, dukkaninau sun amince da bukatar kara domin samar da adalci.

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Ya ce akwai bukatar kowanne bangare dake cikin shari’ar da ya tsaya a matsayin da yake tun da farko tunda batun yana gaban Kotun koli, kamar yadda babbar Kotun tarayya ta ba da umarni a ranar 13/6/2024 a cikin kara mai lamba 13/6/2024. FHC/KN/CS/182/2024.”

Mai shari’a Abang, da yake ba da umarnin, ya jaddada cewa sun karbi rokon mai kara saboda ya cika dukkan sharuddan doka da ake bukata don samun agajin da ake nema.

Ya yi nuni da cewa, an riga an shigar da kara mai inganci a gaban kotun koli, wanda ke karfafa bukatar kiyaye abin da ya shafi shari’ar. Bugu da ƙari, Kotun Daukaka Kara ta amince da haƙƙin kariyar da mai kara ke da shi, la’akari da cewa yana kan sarautar tsahon shekaru biyar kafin a cire shi.

“A ganina, Ya cancanci a ba shi kariya har zuwa lokacin da Kotun Koli za ta yanke hukunci,” Abang ya yanke hukunci.

Kotun ta hana wadanda ake kara aiwatar da hukuncin da aka yanke ranar 10 ga watan Janairu wanda ya soke rusa masarautun da gwamnatin jihar Kano ta yi. Har ila yau, ta ba da umarni, tare da ci gaba da gudanar da harkokin mulki har sai Kotun Koli ta yanke hukunci na karshe.

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Kotun ta umurci mai kara da ya shigar da karar cikin kwanaki 14 a gaban kotu domin a biya wadanda ake kara diyya idan ba a ba da umarnin ba.

Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ranar 10 ga watan Janairu ya soke hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke a baya, wadda ta soke dokar masarautar Kano ta 2024. Wannan doka ta sake sabbin masarautu guda biyar tare da mayar da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...