Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan shinkafa miliyan daya a dukkanin kananan hukumomi 774 wanda kudinsu ya kai N16bn .

Sama da ‘yan Najeriya miliyan daya a fadin kasar za su samu buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 10 kowannen su yayin da gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta kaddamar da shirin samar da abinci na kasa na shekara ta 2025 a ranar Alhamis wanda ya kai Naira biliyan 16.

Da yake jawabi a wajen bikin a Kano, shugaban gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce rabon buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 10 ga talakawa da marasa galihu miliyan 1 a Najeriya na daga cikin kudirin kamfanin Dangote da gidauniyar na rage talauci a cikin al’umma.

Dangote, wanda ya samu wakilcin ‘yarsa Maryama Aliko Dangote ya ce: “Wannan shiri na shekara shekara, wanda ya kunshi tausayi, hadin kai, da kuma daukar nauyi, wani bangare ne na magance kalubalen tattalin arzikin da kasarmu ke fuskanta a halin yanzu. Hakan na nuni da kudurinmu na tallafawa al’ummarmu.”

InShot 20250309 102403344
Talla

Ya ce gidauniyar ta fara rabon kayayyakin ne a jihar Kano, daga nan kuma za ta tsallaka zuwa wasu jihohi, tare da tabbatar da cewa abincin ya kai ga wadanda suka fi bukata a dukkan kananan hukumomin Najeriya.

Alhaji Dangote, wanda shi ne hamshakin attajiri a Afirka, ya ce abinci ya kasance abin bukata na dan Adam, kuma wannan ne ya sa gidauniyar Aliko Dangote ta rungumi dabi’ar fara shirin rabon abinci a fadin Jihohin Nigeria .

Ya kara da cewa, “Muna hada kai da gwamnatocin jihohi don tabbatar da cewa abincin ya kai ga marasa galihu a kowace jiha.”

” Ina yabawa gwamnati a dukkanin matakai na kokarin shawo kan matsalar abinci. Ina da yakinin cewa idan lokaci ya yi, za mu shawo kan wadannan kalubale, don haka mu marawa gwamnati baya don cimma burinta na kyautata rayuwa ga ‘yan Najeriya,” inji shi.

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Gwamna Abba K. Yusuf na jihar Kano, wanda ya kaddamar da shirin samar da abinci na shekara-shekara na kasa, ya ce tallafin na nuna jajircewar Alhaji Aliko Dangote wajen magance talauci da yunwa a Najeriya.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kwamared Aminu Abdulsalam Gworzo ya ce za a raba buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 10, ga mutane 120,000 a fadin kananan hukumomin jihar 44.

Ya bayyana Alhaji Aliko Dangote a matsayin mai tausayi , inda ya kara da cewa: “A shekarar da ta gabata makamancin haka ta faru inda shi da kansa ya kaddamar da rabon kayan abinci ga talakawa a wannan wurin.

Domin tabbatar da gaskiya wajen rabon kayayyakin, ya ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da ya kunshi ma’aikatu da suka hada da CSOs da malaman addini da kananan hukumomi da hukumar Hisbah da hukumomin tsaro.

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Da ta ke zantawa da manema labarai, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gidauniyar Aliko Dangote, Zouera Youssoufou, ta ce shirin samar da abinci na shekara-shekara hanya ce ta magance talauci, da kuma tallafa wa gwamnatoci wajen yaki da talauci da yunwa a Najeriya.

Ta ce Alhaji Aliko Dangote yana da sha’awar bayar da agaji kuma ya jajirce wajen ganin an kawar da yunwa ko kuma an rage ta zuwa ga mafi kankanta a Najeriya.

“Za mu je wasu jihohi mu raba kayayyakin, amma mun kaddamar da shirin a Kano,” kamar yadda ta shaida wa manema labarai a gidan gwamnatin Kano, wurin da aka kaddamar da rabon tallafin

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah a Kano, Dr. Mujahid Aminudeen ya godewa gidauniyar Aliko Dangote bisa samar da wannan tallafin, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi koyi da Dangote ta fuskantar ayyukan jin kai.

Ya ce hukumar ta Hisbah za ta tabbatar da cewa kayayyakin sun isa ga wadanda suka chanchanta.

Wakilin talakawa da marasa galihun da suka amfana da tallafin Ibrahim Ahmed ya godewa Alhaji Aliko Dangote, sannan kuma ya yi masa addu’ar Allah ya taimake shi a harkokin kasuwancin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...