Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP, Jafar Sani Bello, ya kalubalanci ƙaramar ministar ilimi, Suwaiba Ahmad, bisa yadda ta nuna adawa da rufe makarantu a watan Ramadan da wasu jihohin Arewacin Najeriya su ka yi .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jafar Sani Bello ya aikowa jaridar Kadaura24 ranar Alhamis.
Ya ƙalubalanci ƙaramar ministar kan matakin da ta ɗauka na sukar rufe makarantu a wasu jihohin Arewa, yana mai cewa rufe makarantu saboda wani abu da ya shafi addini ba wani sabon abu ba ne a Nigeria.
“Muna buƙatar ta kawo ma na wata hujja kan rufe makarantu har na tsawon kwanaki 104 a shekara waton a kwanakin Asabar da Lahadi 52. Baya ga rufe makarantu da ke yi a ranar bikin Ester Monday da Good Friday. Shin ba ta da masaniya ne game da rufe makarantu da ake yi a Ranae Boxing Day? Ko ta san dalilin yin hakan hakan?”.Jaafar Sani Bello ya tambayi Ministar

Tsohon dan takarar na PDP yana goyon bayan matakin da jihohin Kano, Katsina, Bauchi, da Kebbi su ka ɗauka ne na rufe makarantu a cikin watan Ramadan, inda ya ce kamata ya yi kowanne mai mulki ya fifita buƙatun jama’ar maimakon fifita ra’ayinsa na kashin Kai.
“Hakika, babu wata doka ta halasta rufe makarantu a wannan watan, amma ana zaɓar gwamnatoci ne don biyan buƙatun al’ummar su, ba tare da la’akari da ra’ayi ba. Na yi imanin matsayinta na ƙaramar minista ya nuna irin fahimtar ta game da harkokin mulki da abin da ya kamata ya kasance,” inji shi.
Ya ka da cewa, kasancewar makarantu a bude lokacin Azumin Ramadan na dora wa iyaye nauyi sosai, musamman a kasar da ba ta da tsarin ciyar da dalibai a makarantu.
Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria
Jafar Sani Bello, ya yi martani ga Kalaman da Suwaiba Ahmad ta yi a wani shirin na gidan Talabijin na Channels, inda ya kalubalanci gwamnonin da suka rufe makarantu a jihohinsu saboda watan Ramadana.
Ya na mai tambayar cewa shin shi tsohon shugaban ƙasa Janar Yakubu Gowon da ya ayyana ranar Asabar a matsayin ranar hutu a ina ya samo hakan wanda hakan ya rage kwanaki 52 a shekara.
Ministar ta ba da misali da ƙasar Saudiyya da sauran ƙasashen musulmi da ke buɗe makarantu a cikin watan Ramadan, inda Jaafar Sani ya jaddada cewa ba koyarwar addinin Musulunci ba ce ta tilasta rufe makarantu saboda azumi ba.
Ta kuma nuna damuwa game da ɓata lokacin karatu sakamakon rufe makarantu tare da bayyana cewa ma’aikatar ilimi ta tarayya na tattaunawa da jihohin da abin ya shafa.
Har ila yau, Bello ya ci gaba da cewa, an yanke hukuncin rufe makarantun ne bisa la’akari da al’adun mutanen arewacin Nigeria.