Daga Rahama Umar Kwaru
Matatar mai ta Dangote ta bayyana cewa ta rage farashin man daga Naira N825 zuwa Naira N815 kowacce duk lita .
Sanarwar ta ce Sabon farashin ya fara aiki ne tun daga ranar alhamis 13 Maris 2025.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya ce ya rage farashin man ne sakamakon yadda farashin danyan man ya sauka a kasuwannin duniya.
Idan dai za a iya tunawa Kadaura24 ta kamfanin Dangote ko a ranar 27 ga watan fabarairu sai da Dangote ya rage farashin man fetur bayan karin da aka samu a kwanakin baya.
Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano -Kwamared Waiya
Rahotannin sun nuna yadda masu gidajen mai da dillalan man ke kokawa da yadda Dangote ka rage farashin man a kowanne lokaci.
Punch