Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Shugaban karamar hukumar birni da kewaye, Kwamared Faizu Alfindiki, ya damka Naira miliyan biyu ga ‘yan kasuwar kurmi ‘yan littattafai da ke layin Alhaji Matazu, wadanda gobara tai sanadiyar kone musu shaguna da kayayyaki.
Gwamnan Jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne yai umarnin bayarda kudin domin rage musu radadin abunda ya faru ta karkashin ma’aikatar kananan hukumomi wadda Hon. Murtala Sule Garo ke jagoranta.
Shugaban karamar hukumar, a madadin gwamnatin jahar ya mika sakon jajantawa ga wadanda iftila’in gobara ta afkawa, sannan ya yi kira gare su da su yi hakuri, yana mai cewa gobarar jarrabawa ce daga Allah Madaukakin Sarki.
A jawabansu daban-daban Shugabani da ‘yan Kungiyar Masu sayar da littattafai a Kasuwar ta Kurmi sun yabawa gwamna Ganduje da Shugaban Karamar Hukumar Birni da kewaye Fa’izu Alfindiki bisa yadda Suka Nuna Damuwar su tun Daga Lokacin da iftila’in ya afku, tare da fatan Sauran Shugabani zasu yi koyi da su.
Kadaura24 ta rawaito a Ranar Litinin din data gabata ne kwamaret Fa’izu Alfindiki ya halasci Kasuwar domin jajanta musu tare da yin alkawarin Gwamnati zata tallafa musu domin rage musu radadin halin da Suka tsinci kansu a ciki.