Kun Ko San Aiyukan Hukumar NIMASA ?

Date:

  • Daga Zubaida Abubakar Ahmad
 Hukumar kula da tsaron jiragen ruwa ta Najeriya (NIMASA) ce ke da alhakin kula da tsaron tekun kasar, da ka’idojin aikin ruwa, da hana gurbatar ruwa a cikin teku, aikin bincike da ceto, da kuma tabbatar da tsaro.
 Sauran ayyukan da Hukumar ke gudanarwa su ne haɓaka jigilar kayayyaki da rajistar Kayan da ake shigowa da su ta jiragen ruwa;  horarwa da ba da takaddun shaida ga ma’aikatan jirgin ruwa, da kuma inganta tekunan.
 Har ila yau, hukumar na da alhakin tabbatar da ayyukan da ake gudanarwa a takunan Najeriya, ciki har da kula tattalin arziki Wanda ya dace da dokokin kasa da kasa.
 Wannan ya haɗa da ɗaukar kyawawan ayyuka na ƙasa da ƙasa da waɗanda ke aiki a sashin tekun ƙasar nan.
 Shugaban NIMASA na yanzu shi ne Basir Jamoh, shugaba mai hangen nesa da manufa wanda ya jajirce wajen tabbatar da ganin ya cimma aikin da aka dora masa na ciyar da hanyoyin ruwan Najeriya zuwa ga Mataki na gaba.
  Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a wannan dandali don cigaba da Kawo muku Ayyukan Hukumar NIMASA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudin 2026 da ya kai N1.368 tiriliyan

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar...

Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Nigeria – Abba Anwar

Daga Abba Anwar Wani babban abin lura game da rayuwar...

Kungiyar Ɗaliban Mariri ta gudanar da aikin duba marasa Lafiya kyauta a yankin

Daga Abdallahi Shu'aibu Hayewa   Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato...

Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga...