Za mu fara kai masu satar mana wuta kotu- KEDCO

Date:

 

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano, KEDCO ya ce nan ba da daɗewa ba za ta fara kai waɗanda su ke mata satar wuta, musamman ta mita kotu.

Kamfanin ya koka da cewa satar wutar lantarki da kuma haɗa wuta ba bisa ƙa’ida ba wani gagarumin naƙasu ne ga tattalin arzikinsa.

Shugaban kamfanin, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna ya ce da ga yanzu kamfanin ya dena yin afuwa ga duk wanda a ka kama da yi masa zagon ƙasa, in ji ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na KEDCO, Sani Ibrahim Shawai a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Sanarwar ta ƙara da cewa” lokaci ya wuce da za a riƙa zuwan neman alfarmar mu yafewa mutum bayan ya yi mana zagon ƙasa a kan arzikin mu. Duk wanda ya yi mana satar wuta to fa sai dai ya tsinci kansa a kotu.

“Mahukuntan kamfanin nan sun ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa ba a kawowa kamfanin naƙasu wajen ƙoƙarin da ya ke yi na gamsar da abokan harkarsa ba.

“Tuni mu ka fara bibiya domin mu gano masu yi mana haɗin wuta ba bisa ƙa’ida ba da kuma amfani da mita ba tare da ƙa’ida ba, kuma duk wanda muka kama sai ya gurfana a gaba ƙuliya,”

Kamfanin ya kuma yi kira ga abokan harkarsa da su dage su riƙa biyan kuɗin wuta a kan lokaci sannan su riƙa bada bayanai a kan satar wuta.

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...