Daga Rabi’u Hassan Sani
Jami’ar nan mai zaman kanta ta Al-Istiqama dake garin Sumaila ta karɓi Dalibai 100 da gwamnatin jihar Sokoto ta ɗauki nauyin karatun su ƙarkashin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
Ɗaliban da Gwamnatin jihar ta dauki nauyin karatun nasu sun sauka a jami’ar a ranar Asabar domin fara gudanar da karatun su na digiri a fannoni daban-daban.
Yanzu haka dai ɗalibai 37 ne Cikin 100 na daliban Suka iso Jihar Kano daga Jihar Sokoto.
Da ta ke jawabi Shugabar Hukumar bada tallafin karatu ta jihar Sokoto Hajiya Altine Shehu Kajiji ta bayyana cewa wannan ɗaukar nauyin karatun ɗaliban na ɗaya daga cikin abin da gwamnatin jihar Sokoto ta sa a gaba don ganin ‘yan jihar sun samu damar yin karatu a jami’o’in da ke faɗin kasar nan harma da ƙetare.
Ta ce don haka ne gwamnatin jihar ta sanya wa ɗaliban alawus na naira dubu 30,000 ga kowannen su a duk wata don su gudanar da karatun su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
A jawabinsa a ya yin karbar daliban a madadin shuwagabannin jami’ar mataimakin shugaban jami’ar Dakta Kabiru Muhammad, ya bayyana jin daɗin sa tare da jinjina wa gwamnan jihar Sokoto bisa wannan namijin aiki tare da jan hankalin dalibai da su himmatu wajen koyarwar Jami’ar wanda ta maida hankali wajen bada tarbiyya da koyarwar Addinin musulunci baya ga samun kwalayen su na Digiri.
Taron karbar ɗaliban dai ya samu halartar wasu daga cikin shugabannin jami’ar da su ka haɗa da Jami’in gudanarwa na Jami’ar Hassan Abdurrahman, Mai kula da dalibai wato Students affair Musa Sa’adu da sauransu.