Sarkin Gaya ya bada tabbacin bada goyon bayan Hana barace-barace a Kano

Date:

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe
Masarautar Gaya dake jihar Kano ta jadadda kudirin na cigaba da shiga lungu da sako na yankin domin wayar da Kan al’umma muhammancin ilimi ta ko wacece fuska musamman ga yara manyan gobe.
Mai Martaba sarkin Gaya Alhaji Dakta Aliyu Ibrahim na II shine ya bayyana hakan a lokacin daya karbi bakuncin tawagar yan kwaminitin da gwamantin jihar kano ta kafa karkashin jagorancin tsohon sakataran gwamantin jihar Kano Injiniya Rabi’u Suleman Bichi a fadar sa a yau laraba domin dakile yawaitar barace barace a fadin jihar Kano.
Kadaura24 ta rawaito Sarkin yana mai bayyana cewar muddin ilimi ya waita a cikin al’umma za’a samu raguwar mabarata, a don haka ne a cewar sa basa gajiyawa wajan Kai rangadi makarantun Boko da kuma na Islamiyya tare da basu tallafin kayayyakin koyo da koyarwa. Yana Mai nanata cewar tun daga lokacin daya zama sarkin Gaya ya dauki batu ilimi da mahimmaci ya kara da cewar aikin wannan kwaminitin dama yana cikin tsare tsaran masarautar ta Gaya.
 Alhaji Dakta Aliyu Ibrahim na II ya sake tabbatar da cewar zasu yi aiki kafa da kafa da wannan kwaminitin ta hanyar zama da dukkanin hakimai, Dagatai, da kuma masu unguwanni domin nuna musu illar barace-barace da wasu daga cikin al’umma suka dauke ta a matsayin sana’ar su ta yau da kullum dama wadanda suke zuwa daga wasu jahohin kasar nan dama masu zuwa daga kananan hukumomin dake wajan jihar ta kano.
Shi ma da yake nasa jawabin shugaban kwaminitin da gwamantin jihar Kano ta kafa domin dakile barace-baracan a fadin jihar Kano Kuma tsohon sakataran gwamantin jihar Kano Injiniya Rabi’u Suleman Bichi ya bayyana cewar sun kai ziyarar ne domin gabatar da kawunnan su tare shedawa sarkin aiyukan kwaminitin da zai fara aiki nan bada jimawa ba, Injiniya Rabi’u Suleman Bichi ya kara da cewar dukkanin tsare tsaran da ake bukata tun suka kammala domin fara aikin gadan gadan.
Kuma cigaba da cewar kwaminitin yana kunshe ne da mutane daga bangarori daban daban da sukar hadar da Rundunar yan sandan jihar kano, Hukumar Hisba, ma’aikatar Shari’a, ma’aikatar mata da walwalar kananan yara,  Hukumar tsaron ta farin kaya DSS dakuma na Civil Defence, Hukumar yaki da safarar kananan yara, kungiyoyin sa kai dai makamantan su.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...