Kotu ta sanya ranar cigaba da Shari’a tsakanin Gwamnatin Kano da Sarki Aminu Ado Bayero

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

A ranar Laraba ne wata babbar kotun jihar Kano, ta sanya ranar 10 ga Oktoba, domin yanke hukunci kan karar da aka shigar gabanta na neman hana mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado-Bayero gyaran gidan sarki na Nassarawa.

Gwamnatin Jihar Kano da Babban Lauyan Kano da kuma Majalisar Masarautar Kano ne suka shigar da karar ta hannun lauyansu Rilwanu Umar SAN, wanda ya shigar da karar a ranar 12 ga Satumba, 2024.

Masu karar na neman kotu ta hana Alhaji Aminu Ado-Bayero gyara gidan sarki na Nasarawa da ke kan titin zuwa gidan gwamnatin Kano.

Talla

Alhaji Aminu Ado-Bayero dai shi ne wanda ake kara a karar.

A lokacin da aka zo sauraron karar, Lauyan masu kara Habib Akilu, ya shaida wa kotun cewa wanda ake karar ko shi ko wakilansa ba wanda ya halarci zaman kotun.

Sojoji sun bayyana dalilin korar Seaman Abbas daga aikin Soja

Akilu ya gabatar da takardar neman shiga tsakani yana neman a hana wanda ake kara sake ginawa ko canza fasalin gidan sarkin na Nasarawa.

Talla

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta ruwaito cewa, a ranar 13 ga watan Satumba ne kotun ta bayar da umarnin dakatar da wanda ake kara, da wakilansa, daga rushewa, gyarawa, ko sake gina gidan Sarkin na Nasarawa da ke kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar Kano, har zuwa lokacin da za a saurari karar da kuma yanke hukunci a kan Shari’ar.

Kotun ta kuma umurci dukkanin bangarorin da suke cikin karar da su tsaya a yadda suke har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NURTW ta Karrama DMD Karota Auwal Aranposu

Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababa hawa ta jihar...

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...