Matsin Rayuwa: Ya kamata shugabannin a Nigeriya su gaggauta samawa al’umma mafita – Umar Ahmad Uran

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Global Community for Human Rights Network ta bukaci masu ruwa da tsaki a Nigeria da su waiwayin halin da talakawan kasar ke ciki na matsin rayuwa tun bayan janye tallafin man fitir da Shugaba Tinubu ya yi .

“Talakan kasar nan ya shiga tsakamai wuya sakamakon tashin kayayakin amfanin yau da kullum, wanda hakan yasa wasu ke kwana da yunwa”.

Talla

Shugaban kungiyar na shiyyar Gezawa da Gabasawa a jihar kano Umar Ahmad Uran ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilin kadaura24 a ofishin sa da ke karamar hukumar gezawa.

Ya kara da cewa yanzu sun fi samu yawaitar korafe-korafe musamman a bangaran ma’aurata, inda ya ce ba komai ba ne ya jawo hakan ba sai tsananin matsin rayuwa da al’umma suke ciki.

Majalisar na neman sa kafar wando guda da shugaban ƙasa Tinubu

” Akwai bukatar shugabannin a dukkanin matakai su dauki matakai na gaggawa wadanda za su samarwa da al’umma sauki ko da a fannin kayan abinchi ne tunda shi ne ya zama dole ga kowanne mai rai”.

Haka zalika Umar Ahmad Uran ya ja hankalin ma’aurata musanman Mata dasu rinka yin hakuri da abin da suka samu daga wajan mazajansu a wannan lokacin domin rufawa junansu asiri.

Talla

Daga karshe yace sunan da kyakyawar alaka da sauran kungiyoyi makamantan irin nasu wajan gudanar da aikin su a jihar kano .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...