Muhimmiyar sanarwa daga gwamantin jihar kano ga wadanda suka yi takara a NNPP

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci jami’an gwamnatinsa da suka ajiye mukamansu domin yin takara a zaɓen shugabannin kananan hukumomin dake tafe a jihar, da cewa idan suna bukatar komawa mukamansu suna da damar yin hakan.

Bisa ga sahalewar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ana sanar da daukacin masu rike da mukaman gwamnati da suka sauka daga kan mukaman nasu domin yin takara a zaben Kananan Hukumomi da ke karatowa, amma hakan bata samu ba, kuma suke da sha’awar komawa kan mukamin nasu a yanzu, da su je ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, wato Cabinet Office, daga ranar Talata, 24 ga watan Satumba, shekara ta 2024 domin cike takardun da suka kamata.

Inganta Ilimi: Gwamnan Kano ya rabawa makarantu kujerun Zaman ɗalibai

Hakan kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada Labarai da al’amuran Cikin Gida na jihar Baba Halilu Dantiye ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano.

Talla

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito akwai jami’an gwamnatin da dama da suka ajiye mukamansu domin tsayawa takara kuma ba su sami nasara ba, tun a zaben fidda gwani da jami’ar NNPP ta gudanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ga Kalaman Kwankwaso

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin Sanata Rabiu Musa...

Yadda Kwamishina a gwamnatin Kano ya tsayawa wani dilan ƙwaya aka bada belin sa a kotu

  Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya tsaya...

Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Tinubu

  Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya...

Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC ta yi Sabon Shugabanta na Kasa

  Ministan Jinkai da ba da Agajin Gaggawa, Farfesa Nentawe...