Daga Zara Jamil Isa
Wasu masu gidajen man fetur a jihar Kano sun rufe gidajen man da a dakon karin farashin man fetur.
Rahotanni sun nuna cewa an fara samun dogayen layukan motoci a gidajen mai a kano tun ranar juma’ar data gabata, lamarin ya sake kunno kai a wasu gidajen mai a wasu sassan jihar a ranar Litinin.
Yawancin masu sayar da man a cikin babban birni na jihar nan sun rufe gidajen mai.
wakilin kadaura24 a zagayen da ya gudanar ya gano yadda aka yi jerin gwanon ababan hawa a gidajen mai da ke siyar da Man.
Kananan hukumomin Bichi, Gwarzo ,Tsanyawa da Dawakin tofa ma haka lamarin yake inda rahotanni suka tabbatar da ana siyar da litar man a kan Naira 175 mai makon 165.
Wani direban motar ‘yan kasuwa mai suna Aliyu Ibrahim, ya ce ya kasance a kan layi a daya daga cikin gidajen man a birnin kano na sama da sa’o’i 4.
A makon daya gabata ne shugaban hukumar karbar Ƙorafe – ƙarafe ta jihar kano Barr. Balarabe Mahmoud ya kewaya wasu daga cikin gidajen man domin magance boye man da suke yi,amma dai a wannan karon ma al’umma suna ta zuba idanu don ganin irin matakin da hukumar zata dauka kan wancan zargi da ake yiwa masu gidajen man.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN reshen jihar Kano ta sanar da gwamnati kan wani shiri da wasu masu zaman kansu ke yi na kara farashin man fetur a kasar.
An ruwaito shugaban kungiyar IPMAN reshen jihar Kano, Alhaji Bashir Danmallam yana fadar haka a wata sanarwa da ya fitar kwanan baya a Kano, inda ya ce matakin zai haifar da rikicin mai a kasar.
“Kungiyar ta ga ya zama dole ta sanar da gwamnati don kada ta zargi mambobinmu idan suka kara farashin Man fetur din”.
Al’umma da dama dai na ta yin Allah wadai da wannan matsalar ta rashin mai ,wadda suke tsammanin masu gidan man suna rufe gidan man ne ba don babu man ba.
If you desire to improve your knowledge only keep visiting this web
page and be updated with the latest news update posted here.
Post writing is also a excitement, if you be familiar with after that you can write or elseit is complex to write.
I’m really impressed together with your writing abilities as well as with the structure on your
weblog. Is this a paid subject or did you customize it yourself?
Anyway stay up the excellent quality writing, it is rare to
peer a great blog like this one nowadays..
I am sure this paragraph has touched all the internet people, its really reallygood post on building up new weblog.
Ahrefs account for just $15, semrush account for just $10, Adsply account for just $20, Jarvis account for just $20, adplexity account for just $50 and many group buy account at cheap price