Daga Sani Magaji Garko
Babban Mai binciken kudi na kananan hukumomin jihar Kano Ahmad Tijjani Abdullahi ya ce sanya hanu akan dokar kula da kashe kudaden kananan hukumomi ta shekara ta 2020 wacce gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi zata temaka wajen tabbatar da adalci da kuma bin ka’ida yayi kashe kudaden jamaa.
Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana hakan ne a taron karawa juna sani da aka shiryawa masu binciken kudi na kananan hukumomi 44 da ke nan Kano dokoki da ka’idojin da ke kunshe a sabuwar dokar a Kaduna.
Ya ce an shirya taron ne domin bayyanawa masu binciken kudi na kananan hukumomi yadda za su bibiyi tsare-tsare kashe kudaden alumma a kananan hukumomi 44 da kuma temakawa shugabanni yin adalci a ayyukan su.
“Taron karawa juna sanin ya zo ne sakamakon kudirin dokar binciken kashe kudaden alumma ta shekara ta 2020 wacce majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ita Kuma zababban gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sanyawa hanu da nufin Bangaren binciken kudi ya tsaya da kafar sa ya kuma ci gashin kansa”.
Ahmad Abdullahi ya kuma yabawa Ganduje dangane da yadda ya sanyawa dokar hanu, ya kuma sahale aka gudanar da taron karawa juna sanin domin amfanin maaikata, kana ya kuma yabawa majalisar dokokin jihar Kano da kwamitin ta Mai kula da dukiyar alumma karkashin jagorancin Alhaji Salisu Ibrahim Doguwa bisa gudun mowar da suka bayar don samun nasarar dokar.
A jawabinsa yayin taron, shugaban kwamitin kula da dukiyoyin al’umma na majalisar dokokin jihar Kano Salisu Ibrahim Doguwa ya bukaci babbar Mai binciken kudi ta jihar Hajiya Amina Inuwa Sa’id da babban Mai binciken kudi na kananan hukumomi da su sake shirya ire-iren wadannan taruka da nufin horar da maaikatan su ka’idojin da ke kunshe cikin dokar.
Ya ce taron zai Kara zaburar da masu binciken kudi a jiha da ma masu ruwa da tsaki aiwatar da budaddiyar gwamnati da kuma bin ka’ida wajen kula da dukiyar alumma.
Tunda farko a jawabinsa, kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu na jihar Kano Murtala Sule Garo Wanda babban sakataren maaikatar Alhaji Ibrahim Ahmad Sagagi ya wakilta ya ce maaikatar zata sake shirya makamancin taron da nufin sake horar da masu binciken kudi dabarun gudanar da ayyukan su domin samun sakamako Mai ma’ana.
A yayin taron wadanda sukayi jawabi sun hada da shugaban taron Ali Ben Musa da tsohon shugaban Mai binciken kudi na jiha Muhammad Ibrahim Faruk da babbar Mai binciken kudi ta jiha Amina Inuwa Sa’id da shugaban Shirin SIFTAS a Kano Malam Imam Inuwa Gwale da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kashe kudaden jamaa a nan Kano.