Yadda muka sha matsin lamba kan mu sa INEC ta soke zaɓen shugaban ƙasa na 2023 – Abdussalami

Date:

 

 

Kwamitin tabbatar da zaman lafiya na kasa a jiya Juma’a ya bayyana yadda wasu magoya bayan jam’iyyu da daidaikun mutane suka dinga shirya manuba a yayin zaban shugaban kasa na 2023, inda kwamitin ya bayyana yadda ya dinga shan matsin lamba kan sanya hukumar zabe ta dakatar da tattara sakamakon zaben ko ta soke shi gaba daya.

Kwamitin, wanda tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (Mai Ritaya) ke jagoranta ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a yayin gabatar da rahotansa mai shafuka 106 kan zaben shekarar 2023.

Kafin gabatar da rahotan ga jama’a, kwamitin tun da farko ya gana da shugaban hukumar zabe, Farfesa Mahmood Yakubu da sauran shugabannin hukumar inda suka yi musu bayani kan shirin zaben Gwamna a jihohin Edo da Ondo.

An zargi Hadimin Gwamnan Kano da yada labarin karya kan ganawar Sanata Barau da tsaffin shugabannin LG

Mambobin kwamitin dai sun hada da: Sarkin Musulmai, Alhaji Sa’ad Abubakar na III da Bishop Mattew Kuka da Alhaji Aliko Dangote da Femi Otedola da sauransu.

Wani bangare na rahotan ya ce, “A yayin da ranar zabe ke kusanta, hamayya da mayar da martani sun zafafa. Kwamitin NPC ya karbi kiran waya da dama kan neman a bukaci hukumar INEC ta hau saiti. An kira shugaban kwamitin da wasu mambobi inda aka dinga neman agajin kwamitin na NPC.

“Wasu daga cikin abinda ake nema shi ne kwamitin ya bukaci INEC ta dakatar da tattara sakamakon zabe saboda akwai rahotannin sama ka’idoji da rashin biyayya ga dokar zabe. Wasu na cewa ba a bi ƙa’idojin da aka shimfida na yarjejeniyar zaman lafiya ba, don haka yakamata a soke zaben gabaɗayansa.

Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APCn Kano

“Wasu daga cikin masu sharhi sun nemi kwamitin ya dakatar da sanar da sakamakon zaɓen saboda batun kashi 25 na kuri’u a babban birnin tarayya Abuja”.

Sai dai rahotan kwamitin ya ce, bashi da karfin sanyawa ko shiga hurumin hukumar dake da alhakin shirya zaɓe.

Daily Nigerian

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...

Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta haramta auren jinsi

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta...