Daga Rahama Umar Kwaru
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nigeria, Sanata Barau Jibrin, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa sanya hannu a kan kudirin dokar da ta samar da Hukumar Raya yankin Arewa maso Yamma, wanda shi ne ya gabatar a a gaban majalisar .
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, Mataimakin Shugaban Majalisar ya ce hukumar idan aka kafa ta, za ta taimaka wajen samar da ci gaba a fadin Jihohi bakwai da ke shiyyar – Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa Sokoto da Zamfara.

Ya ce: “A yau ne shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hannu a kan kudirin dokar hukumar raya yankin Arewa maso Yamma da ni ne na gabatar da kudirin a gaban majalisa.
Waɗanda Suka Yi Zanga-Zanga A 2012 Na Kokarin Danne Haƙƙin Yan Nigeria — Atiku
“Hukumar za ta taimaka wajen bunkasa yankunan ta fuskar abubuwan more rayuwa da ake bukata, samar da abinci da sauran ci gaba.