A Shirye nake na inganta harkokin noma da Kasuwanci a K/H Garun Mallam – Mudassir Dakasoye

Date:

Daga Safyan Dantala Jobawa
Shugaban majalisar karamar hukumar Garun mallam Mudansur Aliyu Dakasoye ya bayyana cewa a Shirye yake ya inganta harkokin noma da Kasuwanci a Karamar Hukumar Garun Mallam.
Ya bayyana hakan ne lokacin taron mika tsarin bukatun al’ummar karamar hukumar na shekarar 2021/2022 wanda ya gudana a sakatariyar karamar hukumar a Wani bangare na tattara ra’ayin al’umma Dangane da abun da suke bukata a saka musu Cikin Kasafin kudin Shekara ta 2022.
Mudassir dakasoye  ya ce babban burinsa ya ga  ya fadada fannin kasuwanci tare da inganta sha’anin noma irin na zamani a fadin Karamar Hukumar sa.
Daga bisani, ya lisafto wasu manyan aiyuka da ake aiwatarwa a wasu mazabun yankin tare da karfafawa da fadada kasuwar kayan gona ta  Kwanar Gafan, kana da kirkiro wasu kananan kasuwanni a yankin don kawar da zaman tsegumi ga matasa.
Shugaban Karamar Hukumar ta Garun Mallam ya gode wa gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa irin tagomashin da ya ke baiwa majalisar karamar hukumar Garun mallam.
Tun da fari, shugaban ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Kano, Murtala Sule Garo wanda ya sami wakilcin mataimakin darakta Sashin kididdaga da tsare-tsare na ma’aikatar kananan hukumomi Engr Yunusa Abdullahi, ya bayyana karamar hukumar Garun mallam a sahun farko wajen maida hankali don kawo muhimman aiyukan cigaba tare da samar da aiyukan yi ga al’ummarta.
 Murtala Sule Garo ya bukaci al’ummar yankin da su godewa shugaban karamar hukumar bisa namijin kokarin da ya ke yi don ganin kawo aiyuka a yankinsa, Sannan ya gode wa al’ummar karamar hukumar bisa irin goyan bayan da hadin kan da suke baiwa gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje.
 Kwamishinan ya bayyana cewa ya  gamsu da irin aikace-aikacen da kungiyar cigaban Karamar hukumar Garun mallam karkashin jagorancin Dallatun Garun mallam Awaisu Umar Usman na ganin yadda suke zakulo aiyukan da al’umma ke bukata don gabatar da su ga gwamnati.
Da ya ke mika bukatun al’umma, shugaban gamayyar kungiyoyin, Awaisu Umar Usman ya bukaci gwamnati da ta rinka la’akari da irin tsare-tsaren da kungiyoyin cigaba yankuna ke gabatar wa wanda ya bayyana su a matsayin sune aiyukan da jama’a suka fi damuwa da su.
 A karshe, Awaisu Umar ya yi kira ga gwamnatin jihar kano da ta dubi irin halin da manoman yankin karamar hukumar  Garun mallam da takwarorunsu na Kura da kuma Bunkure za su shiga na samun tsekon ruwan kogin Hadejiya da Jama’are wanda hakan na iya haifar da karancin abinci da kuma jefa wasu cikin mawuyacin hali.
Taron mika bukatun jama’ar Karamar hukumar na shekara ta 2021/2022 ya sami halartar daraktan kudi da mulki, Alh Shazali Fagge da Ajiyan Rano hakimin Garun mallam Alh Lawan Abubakar Madaki sai shugaban kansiloli Hon Usman Mu’azu da Dagatai,Limamai, malamai da shuwagabannin al’ummomi da sauran jama’a na loko da sako na karamar hukumar ta Garun mallam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...