Daga Zakaria Adam Jigirya
Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji, Kano a Majalisar Wakilai ya fara aiki a hukumance a matsayin sabon Shugaban Kwamitin Gidaje da Muhalli na Majalisar.
Sabon shugaban kwamitin Gidajen ya kuma jagoranci tattaunawar kwamitin ta farko a matsayin shugabansa, inda suka tattauna muhimman ƙudurori da tsare-tsaren da kwamitin zai sa a gaba.
Kotu Ta Rushe Kwamitin da Gwamnan Abba Kabir ya Kafa Don Bincikar Ganduje
Wasu daga cikin ayyukan kwamitin sun ƙunshi sa ido kan ayyukan dukkan hukumomi da ma’aikatun gwamnati da ke ɓangaren gidaje da kuma kasafin kuɗaɗensu, harkokin gidaje da batutuwan da suka shafe su, ayyukan gidaje da kuma dokokinsa, harkar samar da kuɗaɗe domin gina gidaje da kuma aiwatar da gine-ginen da kuma abubuwan da suka shafi muhalli.
Ɗan majalisar ya gode wa Shugaban Majalisar saboda ba shi wannan muƙamin, inda ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa tare da sauran mambobin kwamitin da dukkan masu ruwa da tsaki a ɓangaren gidaje da muhalli don ganin sun ba mara ɗa kunya.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Hon. Abdulmumini Jibril Kofa ya taba zama shugaban hukumar samar da gida ta tarayya.
Ga hotunan yadda zaman kwamitin ya Kasance