Kotu Ta Rushe Kwamitin da Gwamnan Abba Kabir ya Kafa Don Bincikar Ganduje

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya dake zaman ta a Kano, ya baiwa Justis Faruk Adamu da Mai shari’a Zuwaira Yusuf, alkalan babbar kotun jihar Kano wa’adin sa’o’i 48 da su yi murabus daga shugabancin kwamitin binciken almundahana da kadarorin gwamnati da kuma tashe-tashen hankula na siyasa, wadanda gwamnatin jihar kano ta kafa.

Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis a karar da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shigar, mai shari’a Amobeda, ya ce hukumar ta kula da harkokin Shari’a ta kasa zata dakatar da biyan duk wani albashi da alawus-alawus da ake yi biyan alkalan biyu daga hadakar asusun shigarta idan har suka gaza bi umarnin kotun.

Talla

Daily trust ta ruwaito cewa, a ranar 4 ga watan Afrilu ne Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da kwamitocin binciken shari’ar guda biyu karkashin jagorancin Mai Shari’a Adamu da Yusuf, domin gudanar da bincike a kan almubazzaranci da dukiyar jama’a, tashe-tashen hankulan siyasa da kuma wadanda suka bace daga shekarar 2015 zuwa yanzu. 2023.

Rikicin Masarautar Kano: Alkali Ya Hana Lauyoyin Magana da Jaridu

Mai shari’a Amobeda ya bayar da umarnin cewa alkalan su daina gudanar da ayyukan zartarwa da gwamnan ya ba su a cikin kotuna wanda ke nufin yanke hukunci a tsakanin mutane da hukumomi a jihar.

Kotun ta kuma bayyana cewa gwamnan ba shi da hurumin nadawa da kuma rantsar da su a matsayin shugabannin hukumar bincike, ofishin da ya kamata kwamishinoni su gudanar da shi.

Kotun ta kuma bayyana cewa, duba da hukuncin da Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya yanke na cewa EFCC da ICPC ne kawai za su iya bincikar tsohon gwamnan, ya ce abun da gwamnan ya yi na kafa kwamitin da zai binciki tsohuwar gwamnatin mai kara cin fuska ne a ga alfarmar bangaren Shari’a .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...