Daga Samira Hassan
Kantomar karamar hukumar Wudil Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ta bukaci Matasa da su zamu masu juriya a yayin da suka sami wata dama ta hidimtawa Nigeria da al’ummar cikinta
” Idan kuka zama masu juri da Kishin kasar ku babu shakka zaku zama abun alfahari ga kasar ku da al’ummar da kuka fito daga cikin su”.
Hajiya Bilkisu Indabo ta bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci wasu matasa yan asalin karamar hukumar Wudil da suka sami aikin soji domin yi musu sallama a barikin sojoji ta Bokavo dake kano.
Gwamnatin Kano ta cimma matsaya tsakaninta da yan kwangilar 5 kilomita a kananan hukumomin jihar
” Aikin Soja aiki ne da zaka taimaki al’ummar kasar ka baki daya, don haka aikin yana bukatar juriya da sadaukar da akai don kaiwa ga gaci”.
“Yau kenan yayin da na sake kai ziyara zuwa Barikin Bokavo domin yin sallama da ƴaƴan Ƙaramar Hukumar Wudil waƴenda zasu tafi horaswa na aikin soja (Military Training) a Jaji, Jihar Kaduna”.
” Za mu taimaka muku da duk abun da kuke bukata, saboda ku sami kyakykyawan yanayin da za ku Mai da hankali wajen daukar horon da za a baku” a cewar Bilkisu Indabo
Ta bukaci matasan da su zama Jakadun karamar hukumar Wudil da jihar kano na gari yayin da suke daukar horo da Kuma bayan kama aiki, don kare kimar al’ummar su a idon duniya.
Ga hotunan ziyarar da Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ta kai wa matasan