Gwamnatin Kano ta cimma matsaya tsakaninta da yan kwangilar 5 kilomita a kananan hukumomin jihar

Date:

Daga Sani Danbala Gwarzo

 

Gwamnatin jihar Kano ta kammala shirin kammala aiyukan titinan karkara mai tsawon kilomita 5 da aka yi watsi da shi a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Laraba bayan kammala wani taro da ‘yan kwangilar da ke gudanar da ayyukan a gidan gwamnati.

Ayyukan na kilomita biyar-biyar da aka warewa miliyoyin nairori tsohon gwamna, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ne ya bayar da su a lokacin gwamnatin sa, kuma tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi watsi da su.

Talla

Da yake ganawa da ‘yan kwangilar, Gwamna Yusuf ya yabawa ‘yan kwangilar kan yadda suka amsa kira a kan lokaci, ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa ta kudirci aniyar kammala duk aiyukan da tsohuwar gwamnatin Kwankwaso ta faro don cigaba al’ummar jihar Kano.

Gwamnan Kano ya nuna damuwa kan aiyukan hukumomin KAROTA da REMASAB

Muhimman batutuwan da aka cimma yayin taron sun hada da Komawar yan kwangilar baki aiki nan da mako guda don kammala aikin.

Sauran su ne umarnin gaggawa da aka baiwa ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta Jiha domin warware matsalolin da ake fuskanta na biyan diyya.

“An yanke shawarar cewa ‘yan kwangilar za su je bankunan su domin karbar kashi 30 cikin 100 na kudaden da aka ware wa aikin, amma ga wadanda basu karɓi na su tun da farko ba.

“An kuma warware matsalar hauhawar farashin kayayyakin gine-gine da aka samu, inda gwamnati ta amince za ta sake duba farashin sauran kayayyakin da aike aikin da su .

“An kuma amince da cewa gwamnati za ta fitar da tsarin da zata rika biyan yan kwangilar a kowane wata, ta yadda ba za sami tsaiko ba. Don haka aka umarci duk dan kwangilar da ya amince da sabon tsarin da ya koma bakin aiki nan da mako guda ko ya rasa damar” .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...