Yan bindigar da suka yi garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara sun bukaci a biya kudin fansar ta Naira biliyan daya.
Majiyar Aminiya a kauyen Kahutu, inda aka yi garkuwa da Hajiya Hauwa’u Adamu, ya bayyana cewa masu garkuwar sun kira iyalan ta waya suna neman kudin tare da shaida musu cewa babu abin da ya same ta.
Majiyar, wadda ke da kusanci da iyalan dattituwar, ta ce ’yan bindigar “sun kira ne ta wayar wata ’yar gidan a lokacin da suka kai harin da suka sace Hajiya.

“Sun nemi a biya kudin fansa Naira biliyan daya, amma bayan tattaunawa da wani dan gidan suka rage kudin zuwa miliyan N900.
Da farko sun nemi tattaunawa ne da Rarara, amma kasancewar ba shi da lafiya tun bayan da suka sace ta, sai suka amince su yi magana da wani dan gidan.
Rikicin masarautar Kano: Abun da ya faru a zaman kotu na yau talata
“Sun tabbatar wa iyalan cewa Hajiya na cikin koshin lafiya kuma za su sake ta da zarar an biya kudin.
“ Cikin dan kankanin lokaci suka yi tattaunawar kuma har yanzu ba su sake kira ba.
“Amma duk hakan ina da yakikin ana ci gaba da tattaunawa da su.
“Iyalan na jiran ’yan bindigar su sake kira, a ci gaba da tattaunawa,” in ji majiyar, wadda ke da kusanci da gidansu Rarara.