Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mamallaka manhajar Tapswap da ke mining din ta sun bayyana cewa sun dage ranar kaddamar da ita.
Jarida PUNCH ta ruwaito shugaban sashin sadarwa na kamfanin, John Robbin ne ya bayyana hakan a wata sadarwa da ya fitar.
Dan majalisar Nasarawa ya tasamma warware matsalar asibiti a wasu unguwannin yankin
Matasa da yawa a Nigeria dai sun rungumi mining, tun bayan da wasu matasan suka sami kudade masu yawa a Notcoin.

Kafin wannan lokacin a baya kamfanin ya sanar da cewa ranar da zai kaddamar dashi za ta kasance ranar 1 ga Yuli bayan sun kasa gatabar dashi bisa yawan masu yin wasan.
Har Izuwa wannan lokaci kamfanin bai bayyana ranar da zai kaddamar da Tapswap din ba.