Gwamnan Kano ya nuna damuwa kan aiyukan hukumomin KAROTA da REMASAB

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan yadda ma’aikatun tsaftar muhalli da ta karota ke gudanar da ayyukansu a jihar.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, gwamnan ya umarci ma’aikatun biyu su gabatar da cikakken bayanan kayayyakin aikinsu domin tabbatar da ingancinsu.

Gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan wata ziyarar ba-zata da ya kai hukumomin, inda ya tarar da gazawar ma’aikatun tare da jami’an hukumomin.

Gwamnan Kano ya kaddama biyan hakkokin yan fansho a karo na biyu

Abba Kabir ya nuna damuwarsa kan yadda hukumomin ke gudanar da ayyukansu, duk da irin kuɗin da ya ce gwmnati na zubawa a ma’aikatun”, in ji sanarwar.

A hukumar tsaftar muhalli ta jihar, gwamnan ya tarar da motocin kwashe shara bakwai ne kawai ke aiki daga cikin 30 da hukumar ke da su, kamar yadda ya samu motocin loda wa manyan motoci (felloda) uku ne kawai ke aiki daga cikin 15 da ma’aikatar ke da su.

Sanarwar ta cea lokacin ziyarar an shaida wa gwamnan cewa ma’aikatan dindindin 10 ne kawai hukumar ke da su, yayin da sauran duka na-wucin gadi ne.

Mafi ƙarancin albashi: NLC ta Mayarwa da Gwamnonin Nigeria Martani

Abba Kabir ya kuma nuna damuwarsa kan halin da ma’aikatan wucin gadin suke ciki, wanda ya bayyana da zalunci ne mutum ya yi shekara 20 a matsayin ma’aikacin wucin-gadi.

Haka kuma a ma’aikatar kula da dokokin titi ta Karota, gwamna ya tarar da motoci masu yawa da suka lalace.

Inda ya buƙaci hukumar ta gaggauta kai masa cikakken rahoton motocin da ma’aikatar ke da su

Abba Kabir ya ce yadda gwamnati ke zuba makudan kuɗi a hukumar tsaftar muhallin a nuna irin muradin da gwamnati ke da shi wajen tabbatar da tsaftar muhalli, to amma ya ce hukumar ta gaza yin abin da ya dace

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...