Gwamnan Kano ya kaddama biyan hakkokin yan fansho a karo na biyu

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da biyan kudaden Garatutin na wadanda suka kammala aikin gwamnati da kuma wadanda suka rasu a matakin jiha da kananan hukumomi.

Kimanin mutane dubu hudu ne za su amfana a wannan karon, inda aka ware Naira biliyan 5 domin rawaba ga kanana da manyan yan fansho a jihar .

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, ya ce gwamna Yusuf ya bayyana yadda gwamnatin ke ci gaba da kokarin magance matsalolin ‘yan fansho a jihar.

SMEs : Sama Da Kashi 70 Na Mambobinmu Sun Sami Tallafin Dubu Hamsin Hamsin – Nassi.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa Gwamna Yusuf ya bayyana fara fitar da Naira biliyan 6 a watan Nuwamba 2023 don biyan hakkokin wadanda suka gama aikin wadanda gwamnatin da ta shuɗe ta kasa biyansu.

Gwamna Yusuf a lokacin da yake kaddamar da Kashi na biyu na biyan hakkokin yan fanshon, ya bayyana cewa mawuyacin halin da gwamnatin Ganduje ta sanya su ne ya tilasta wa gwamnatin sa Fara rage musu kudaden.

El-Rufa’i ya maka majalisar dokokin jihar Kaduna a Kotu

“Kashi na farko an samu nasarar ware Naira biliyan 6 don biyan kudaden yan fansho 5,333 da suka yi ritaya da kuma wadanda suka mutu da suka hada da wadanda suka yi ritaya a jihohi da kananan hukumomi da iyalan ma’aikatan gwamnati da suka rasu.

“Wannan kashi na biyu na Naira biliyan 5, an ware shi ne da nufin biyan bashin fansho da Iyalan wadanda suka rasu su 4,000.

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa biyan yan fanshon hakkokin su na daga cikin alkawuran da ya yi yakin neman zabe da su a Shekarar 2024.

Kungiyar ’yan fansho ta kasa ta amince da Gwamna Yusuf a matsayin Gwamnan da ya fi kowanne gwamna kaunar yan fansho a 2024 saboda jajircewarsa wajen fitar da su daga halin da su ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...