Daga Umar Sani Kofar Na’isa
Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu, a ranar Alhamis ya kaddamar da rabon hatsi iri-iri domin tallafawa al’ummar jihar don su sami damar gudanar da azumin watan Ramadana cikin walwala.
A wajen bikin da aka yi a Birnin Kebbi, Kwamared, Nasiru Idris, ya ce ya bada tallafin kayan abinchin ne domin Aiwatar da manufofin gwamnatinsa na jin kan al’ummar jihar.
A cewarsa, rabon hatsin shima wani mataki ne na wucin gadi na samar da tallafi ga al’ummar jihar baki daya.
Cin Hanci: Yan Sanda Sun Gurfanar da Jarumar Kannywood, Amal, a Gaban Kotu
Ya kuma umurci duk wadanda aka damka wa rabon hatsin da su tabbatar sun gudanar da aikin rabon hatsin ga daukacin al’ummar jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkokin kafafen sada zumunta Aliyu Bandado Argungun ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Gwamna Nasir ya gargadi kwamitocin rabon kayayyaki a dukkan matakai kan duk wani nau’i na rashin gaskiya Sannan kuma ya hore su dasu guji nuna wariya wariyar siyasa yayin rabon.
Dalilin Da Yasa ’Yan Sanda Suka Nemi Murja Kunya Ta Biya Su Diyyar Naira Dubu 500
Ya kuma yi gargadin cewa duk wani jami’in gwamnati da aka samu yana karkatar da hatsin, za a hukunta shi sosai, wanda zai kai ga tsige shi daga mukaminsa.
Tun da farko kwamishinan noma na jihar Alhaji Shehu Mu’azu ya yabawa gwamnan bisa amincewa da sayan buhunan buhuna hatsin iri-iri domin jin dadin al’ummar jihar.
Ya ce tuni aka aike da hatsin a dukkanin kananan hukumomin 21 dake jihar domin rabawa lungu da Sako na jihar Kebbi.
Hatsin da aka saya don rabawa ga al’ummar jihar a matsayin tallafin azumin watan Ramadan sun hadar da Gero, dawa da shinkafa.