Ya Kamata Hukumar Kwastam ta Sakarwa Yan Kasuwa Mara – Sarkin Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya shawarci hukumar hana fasa kwauri ta kasa (custom) da su kyale yan kasuwa su rinka gudanar da harkokin kasuwancin su ba tare da tsare musu kayansu ba mutukar basu karya doka ba.

Sarkin yayi wannan Kira ne a yayin daya karbi bakuncin mataimakiyar babban shugaban hukumar custom ta kasa Queen Ogbudu da tawagarta a fadar sa.

Dalilin da Yasa Ake Shirin Yanke Wutar Lantarki a Fadar Shugaban Nigeria

Alhaji Aminu Ado Bayero Wanda ya bayyana cewa a baya jami’an hukumar custom suna shiga kasuwa su karbewa ‘yan kasuwa kaya ba bisa kakida ba, amman yanzu yaji dadi da ba’a karbe musu kayan.

Haka kuma sarkin yayi kira ga jami’an hukumar custom din dasu zauna da yan kasuwa domin wayar da kan su akan irin kayan da hukumar suke so a shigo dasu domin cigaban yan kasuwar.

Barazanar Tsaro: Karamar hukumar Gwarzo ta Nemi Hadin Kan Jami’an Tsaro

A nata jawabin mataimakiyar Babban Kwamandan Hukumar Custom ta kasa mai kula da shiyar kano da Kaduna da Jigawa da kuma katsina tace tazo kano ne domin sanar da sarkin cewa shugaban kasa ya bada umarni da su fitar da kayan abinci domin rabawa al’ummar kasa sakamakon matsin da ake fama dashi.

A wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran masarautar Kano Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24, yace a wani cigaban kuma Mai Martaba Sarkin ya karbi bakoncin tawagar mutanen kasar China karkashin jagorancin Mr. Lee Zhong, sai kuma bakoncin shugaban makarantar kwalejin aikin gona ta kasa dake jihar kano karkashin jagorancin Dakta Muhammad Yusha’u Gwaram a fadar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...

Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malamin addinin musulunci a kano...