Dalilin da Yasa Ake Shirin Yanke Wutar Lantarki a Fadar Shugaban Nigeria

Date:

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta sauke nauyin bashin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) saboda gudun yanke wa Fadar Shugaban Kasar wutar lantarki.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya ce za a biya bashin kuɗin wutar lantarkin nan da ƙarshen wannan mako.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kamfanin ya sanya Fadar Shugaban Kasar a cikin jerin wuraren da kantar bashin kuɗin wutar lantarki ya yi wa katutu a babban birnin Nigeria.

Cikakken Bayanin Yadda Shari’ar Murja Kunya ta Gudana Yau a Kotu

Sai dai Mista Bayo ya ce bashin kuɗin wutar lantarkin bai wuce N342, 352, 217.46 ba, sabanin ikirarin da kamfanin na AEDC ya yi na cewa bashin ya kai Naira miliyan 923.

A cikin wata wasika mai kwanan watan 14 ga Fabarairun 2024 da AEDC ya aike wa Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa kuma aka wallafa a wasu gidajen jaridu, yana bin Fadar Shugaban Kasar bashin kuɗin wutar lantarki har Naira miliyan 923.

Barazanar Tsaro: Karamar hukumar Gwarzo ta Nemi Hadin Kan Jami’an Tsaro

A cewar Mista Bayo, “bayan sulhu da aka yi tsakanin bangarorin, an cimma matsaya kuma kowanne ya gamsu, inda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya ba da tabbacin cewa za a biya AEDC bashin kafin karshen wannan makon.

“Saboda haka ana fatan wannan zai zama abin misali ga sauran ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnati da su daidaita da Kamfanin AEDC domin biyan bashin kuɗaɗensu na wutar lantarki.”

 

Daily Trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kisan ɗalibai a Kano: Kwamitin Malamai da Iyayen yara na jihar ya nuna damuwarsa

Daga Abdulhamid Isah D/Z Malam Salisu Abdullahi shugaban kwamitin malamai...

Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari

  Rahotanni daga Katsina na cewa gwamnan jihar Katsina Dikko...

Zargin almundahana: ICPC ku fita daga harkokin Siyasar Kano – Kungiyar Ma’aikatan KANSIEC

Daga Hafsat Abdullahi Darmanawa   Kungiyar ma'akatan wucin gadi da suka...

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...