Rundunar Sojin sama ta kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Kano

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Dakarun Rundunar Sojojin saman Najeriya, NAF da aka tura zuwa Durbunde a karamar hukumar Takai a jihar Kano sun kama wani matashi mai shekaru 35, mai suna Isah Abdul da ake zargi da yin garkuwa da mutane.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, AVM Edward Gabkwet, ya fitar a yau Talata a Abuja.

Gabkwet ya ce an kama shi ne a jiya Litinin da karfe 6:30 na yamma, a wani samame na hadin guiwa da aka yi, biyo bayan sahihan bayanan sirri kan maboyar wanda ake zargin da sauran yaran sa.

Cikakken Bayanin Yadda Shari’ar Murja Kunya ta Gudana Yau a Kotu

Ya ce ƴan kungiyar ne ke da alhakin yin garkuwa da mutane da dama a yankin.

Yanzu-yanzu: Kotu ta bada Umarnin Duba Kwakwalwar Murja Kunya

A cewarsa, wani bincike na farko da aka gudanar ya nuna cewa Isah Abdul ne ke da alhakin sace wani Yakubu Ibrahim Tagaho, wanda aka fi sani da Sarkin Noman Gaya, a ranar 6 ga Afrilu, 2023, daga gidansa da ke kauyen Tagaho a karamar hukumar Takai.

Mista Gabkwet ya ce bayan wata guda aka sako Tagaho bayan da masu garkuwa da mutane suka karbi kudin fansa naira miliyan 30.

Ya ce nan gaba kadan za su miƙa shi ga hukumomin da su ka dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...