Kotu a Kano ta dauki mataki kan hukumar Hisbah, bayan da wasu masu otel sukai karar ta

Date:

Daga Aisha Ibrahim

 

Wata kotu a nan Kano ta yi umarnin kulle asusun bankunan hukumar Hisbah ta jihar Kano, bisa gurfanar da ita da wasu masu Hotel-hotel suka yi a gaban kotun.

 

Sai sai sa yake tabbatar da faruwar hakan a zantawarsa da kafar labarai ta TRT Africa, babbab kwamandan hukumar ta Husbar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce kawo yanzu ba’a sanar da su laifin da suka aikata ba har aka dauki matakin rufe asusun bankunan nasu.

NAHCON ta Bayyana Yadda Saudiyya Ta Rage Kudin Aikin Hajjin Bana

Sheikh Aminu Daurawa ya kuma ce sun san dai an aika musu da wata takardar kotu da take nuni da cewar, akwai wani Hotel da suka taba zuwa aiki wanda suka ce sai sun biya Naira dubu dari bakwai, da kuma wani daban wanda shi ma suka taba zuwa aiki, shi ma zasu biya dubu dari a lokacin.

Sa dai kuma Daurawa ya ce kamata ya yi a fada musu laifin da suka aikata domin su nemi lauya ya shiga cikin batun wanda idan suka kasa kare kansu sai ayi musu hukunci.

Kwamandan Hisban ta Kano ya ce matakin da aka dauka din yanzu haka ya dakatar da ayyukansu kasancewar ba zasu iya taba kudaden asusun su ba.

Yan Kasuwar Canji na Abuja sun sanya ranar rufe Kasuwar

Sheikh Daurawa ya ce yanzu haka ya tura wakili domin yaje ya samu kwamishinan shari’a na jihar Kano, kuma babban lauyan gwamnati Barista Isah Haruna Dederi, domin ba’a sanar musu dalilin daukar matakin rufe asusun bankunan nasu ba.

Idan dai ba’a manta ba a kwanakin baya ne hukumar Hisbar ta jihar Kano, ta rinka kai sumame a Hoto-Hotel, da guraren shakatawa a jihar inda ta rinka kama mutane, da tayi wa take da Operation kau da Badala, lamarin da ya rinka janyo cece-kuce a lokacin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...

Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta haramta auren jinsi

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta...