Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Shugabancin jam’iyyar APC, wadda mulki a Najeriya, ya yi gargadi ga magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kogi na baya-bayan nan, Yahaya Bello, da su guji neman haddasa rudani a jam’iyyar da cewa jam’iyyar tana da shugaba na kasa.
Sa’o’i 48 da Yahaya Bello ya suka daga mulkin jihar Kogi inda ya damka wa sabon gwamnan da aka zaba Usman Ododo, shafukan sada zumunta da muhawara dasauran kafafen intanet sun cika da jita-jitar cewa Bellon na sha’awar kujerar shugabancin jam’iyyar.
Babban Sakataren jam’iyyar na kasa, Felix Morka, shi ne ya yi gargadin a wani taron manema labarai a yau Talata a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
Malam Shekarau ya yi tsokaci Kan Kiran da Ganduje ya yiwa Gwamnan Kano na Komawa APC
A jiya Litinin an ga yadda hotunan tsohon gwamnan na Kogi suka yanyame titunan Abuja har da sakatariyar jam’iyyar da ke babban birnin Najeriyar.
To amma bayan taron babban kwamitin zartarwa na jam’iyyar, sakataren yada labaran jam’iyyar ya fito da sanarwa inda yake jaddada cewa a yanzu akwai wanda yake kan kujerar shugabancin jam’iyyar – wato tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Ya kara da cewa har yanzu Abdullahi Umar Ganduje ne shugabasu saboda haka babu maganar takarar hawa kujerar a yanzu kamar yadda magoya bayan Belloo suke yadawa.
Sabon Gwamnan Kogi Ya Zo da Sabon Salo a Dimokaradiyyar Nigeria
Ya ce kodayake wannan lokaci ne na dumukuradiyya to amma yana gargadin masu yada wadannan hotuna da su bari, domin jam’iyyar na son mayar da hankali ne a kan yadda za ta daidaita al’amuran kasa a yanzu amma ba shugabancinta ba wanda ba su da matsala a kanshi.
Sai dai kuma shi ma tsohon gwamnan jihar ta Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya nesanta kansa daga wannan kamfe da ke danganta shi da neman kujerar shugabancin na APC.
Wata sanarwa da ofishin yada labarai na tsohon gwamnan ya fitar yau Talata ya zargi shugabannin hamayya da wadanda ya kira makiya a cikin jam’iyyar tasu da kitsa wannan abu domin bata sunan tsohon gwamnan.