Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Sabon gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo ya ce ya amince da kafa Ofishin tsohon gwamna a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito daga Ofishin gwamnan jihar ta Kogi.
Sanarwar tace Ofishin tsohon gwamna zai Kasance ne a gidan gwamnatin jihar, kuma zai rika shiga yana gudanar da aiyukan sa na yau da kullum.
Kotun Ƙoli: Shin da gaske ne an kwalla yarjejeniya tsakanin Gwamnan Kano da Tinubu ?
Tsohon gwamnan jihar Kogi da ya sauka kwanan nan Yahaya Bello shi ne zai fara amfani da sabon ofishin, kuma hakan zata bashi damar tsoma baki dakan dukkanin al’amuran da suka shafi gwamnatin jihar karkashin jagorancin sabon gwamnan kogi Usman Ododo, kamar yadda wasikar ta ruwaito.
Malam Shekarau ya yi tsokaci Kan Kiran da Ganduje ya yiwa Gwamnan Kano na Komawa APC
Kafa ofishin tsohon Gwamna zai iya barin jihar cikin rashin tabbas a fannin shari’a domin kafawar ba ta fayyace ainahin hakikanin aikin Ofishin tsohon gwamna ba.