Na yi Nadamar Gudunmawar da Baiwa Gwamnatin Buhari – Mawaki Rarara

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Shahararren mawakin siyasar nan na arewacin Nijeriya Dauda Adamu Abdullahi da aka fi sani da Rarara ya ce gwamnatin da ta gabata ta tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ta lalata kusan kowane bangare na Nigeria.

Rarara a wata ganawa ta musamman da manema labarai a Kano, ya ce ya ba gwamnatin ta Buhari shawarwari daban-daban na yadda za a inganta ayyuka rayuwar al’umma, amma ba ta dauki shawara ko daya daga bangare na ba.

Mawakin da ya yi jawabi mai kama da ya dawo rakiyar gwamnatin da ta shude, ya nuna kamar yana nadamar irin goyon bayan da ya bata.

Talla

Ya yi karin hasken cewa bai samu sisin-kwabo a gwamnatin Buhari ba, ya kara da cewa duk wanda ya ke da hujjar cewa ya samu kudi gwamnatin Buhari ya zo ya nuna.

Gwamnan Kano ya Bayyana Ranar da kashi na 2 na Daliban India da Uganda zasu tashi

Ta fuskar ba da gudunmuwa a wajen kafa sabuwar gwamnatin Tinubu kuwa, mawaki Rarara, ya ce tsoffin gwamnonin Katsina Aminu Masari da na Kano Abdullahi Ganduje ne kadai za su iya daga masa yatsa wajen bada gudunmawa har Tinubu ya sami nasara.

Sai dai Dauda Adamu ya yi karin hasken cewa akwai makiya Tinubu da aka nada mukamai daban-daban a gwamnatinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NURTW ta Karrama DMD Karota Auwal Aranposu

Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababa hawa ta jihar...

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...