Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da gudanar da ayyuka da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar al’ummar jihar.
Da yake jawabi a lokacin da yake duba ayyukan ofishin sa a cikin makonni 3 da suka gabata, a yayin da aka fara taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 7 a gidan gwamnati da ke Kano, gwamnan ya ce an fara gudanar da ayyukan alheri da dama.

Ya bayyana cewa, a cikin wannan lokaci da gwamnatin ta yi nasarar kaddamar da rabon kayan abinci da suka hada da Shinkafa da Masara a mazabun jihar 484.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
PDP ta yi Maryani kan Hukuncin Kotun Kolin Nigeria
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta kuma kaddamar da rabon kayayyakin koyo da koyarwa, Uniform da jakunkuna/Takalmi, baya ga kaddamar da shirin kai dalibai karo na 1 da gwamnati ta dauki nauyin bayar da tallafin karatu a kasashen waje .
Bayan Hukuncin Kotun Kolin Nigeria, Tinubu ya Magantu
“Kashi na biyu na jigilar daliban da za su je Indiya za a ci gaba a ranar Juma’a, yayin da wadanda za su je Uganda za a kai su ranar Lahadi,” in ji gwamnan.
Hakazalika a cewarsa, gwamnati ta yi nasarar kaddamar da auren zawarawa da yan mata 1800 mai suna (Auren Gata) tare da bayar da tallafin kayayyakin daki, kayan abinci, tallafin kudi da sauran kayayyaki ga kowanne daga cikin ma’auratan da nufin tallafa musu.

Alhaji Kabir Yusuf wanda ya bayyana jin dadinsa ga al’ummar jihar bisa goyon baya da addu’o’i, ya kuma yabawa ‘yan jarida bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatinsa, tare da fatan ganin an hakan ya dore.