PDP ta yi Maryani kan Hukuncin Kotun Kolin Nigeria

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta ce hukuncin Kotun Koli a kan korafin da ta shigar tare da dan takararta Atiku Abubakar, a kan nasarar zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babban abin tayar da hankali ne.

Ta ce ‘yan Najeriya har yanzu sun kasa fahimtar yadda kotun koli ta lamunci manyan batutuwan yin jabun takardu da tafka karya da shaidar zur, bisa doron rashin cika ka’idojin shigar da kara.

Talla

Kotun dai ta yanke hukuncin da ya tabbatar da nasarar zaben Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

PDP ta ce ita, da mafi yawan al’ummar Najeriya sun kadu kuma sun ji takaici tare da nuna damuwa a kan tunanin Kotun Kolin, wanda jam’iyyar adawar ta ce ta yi imani ya saba da tanade-tanaden tsarin mulkin Najeriya da kundin dokokin zaben kasar.

Yanzu-Yanzu: Kotun koli ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar da Atiku ya Kalubalanci Nasarar Tinubu

Sanarwar da sakataren yada labaran PDP na kasa, Onarabul Debo Ologunagba ya fitar, babbar jam’iyyar adawar ta jaddada cewa wani abin takaici ne a ce kotun koli ta gaza dabbaka tanade-tanaden doka.

A maimakon haka, sai ta yi watsi da kyakkyawan zaton mafi yawan al’ummar Najeriya wadanda ke kallonta a matsayin gidan samun adalci ta hanyar yanke hukunci a kan batun da ya yi la’akari da dokoki da al’amura na gaskiya a cikin wannan shari’a.

Ta ce da gaske ‘yan Najeriya sun yi tsammanin kotun koli za ta tabbatar kuma ta kare tanade-tanaden tsarin mulkin 1999 wadanda suka fayyace karara batun cancantar dan takara da sharadi mafi karanci da ake bukatar cikawa kafin a ayyana mutum a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Najeriya.

“Musamman la’akari da bukatar doka ta cin kashi 25 na kuri’un da aka kada a birnin Abuja da kuma batutuwan da suka keta dokoki da tsare-tsaren zabe.”

Talla

PDP dai ta ci gaba da zargin jam’iyyar APC mai mulki da tafka almundahana da jirkita sakamakon zabe.

Ta kuma yi ikirarin cewa hukuncin kamar yadda shaida ta bayyana, ya sanyaya kwarin gwiwar da ‘yan Najeriya ke da shi ga bangaren shari’a, musamman a matsayinta kotun koli na madafar karshe ga talaka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...