Daga Aisha Aliyu Umar
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa yana maraba da hukuncin da Kotun Kolin Nigeria karkashin jagorancin Mai Shari’a John I. Okoro ta yanke kan karar zaben shugaban kasa da ‘yan takarar jam’iyyar PDP da na Labour suka shigar, inda suke kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.
” Kotun ta yi adalci ga dukkan batutuwan da aka gabatar domin tantance su a cikin korafe-korafen da suka shafi doka, ba tare da tsoro ko fargaba ba”. A cewar Tinubu

“Ko shakka babu, bisa hukuncin yau, ya nuna cewa tsarin zaben kasar nan da dimokuradiyyarmu sun sami cigaba mara musaltuwa, saboda kwazon alkalai da suka jagoranci lamarin suka nuna wajen yin hukunci na adalci wanda babu son Kai a cikin sa”.
Tinubu ya ce “A yau an sake tabbatar da cewa jam’iyyata mai mulki ta APC, ta samu ‘yancin kai da adalci ga ‘yan Najeriya, wanda tun daga lokacin ne na jagoranci wannan kasa mai girma a cikin rudani na sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsa ba a kasarmu. tarihi a matsayin al’umma” .
Yanzu-Yanzu: Kotun koli ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar da Atiku ya Kalubalanci Nasarar Tinubu
Tare da godiya dinbun godiya ga Allah Madaukakin Sarki, na amince da nasarar shari’a a yau tare da tsananin nauyi da tsananin sha’awar fuskantar manyan kalubalen da ke fuskantar mutanenmu.
Nasarar da aka samu a yau ta kara karfafa niyyata na ci gaba da yi wa daukacin ‘yan Najeriya hidima ba tare da la’akari da bambamcin siyasa, kabila, ko addini ba, sannan zamu zamu masu mutunta ra’ayoyin al’umma don samar da kyakyawan Nigeria.
Tinubu ya yi alkawarin jaddada kokarin sa don samar da ci gaba a Nigeria kuma yace zai ci gaba da yin aiki daga safiya zuwa dare, a kowace rana, don gina Nigeria .
Shugaban kasa Bola Tinubu yace “Dukkanmu ‘yan gida ɗaya ne, kuma a wannan lokacin muna buƙatar mu ci gaba da aiki don gina ƙasarmu tare.
“A cikin kwanaki da watanni masu zuwa, na yi imanin cewa za a daukaka kishin kasa wajen tallafa wa gwamnatinmu don inganta rayuwar ‘yan Nijeriya. A shirye nake in yi maraba da gudummawar da duk ‘yan Najeriya ke bayarwa don haɓakawa da ƙarfafa ci gabanmu tare”.

Ina mika godiya ta ga daukacin ’yan Najeriya kan aikin yi wa kasarmu hidima. Na sake yin alkawarin tsayawa tsayin daka wajen samar da ayyuka da shugabanci na gari.