Daga Isa Ahmad Getso
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nigeria INEC ta cire sunan dan takarar APC Timpre Silva daga jerin sunayen ‘yan takarar gwamnan Bayelsa a zaben da za a yi a ranar 11 -11-23
Kadaura24 ta rawaito Hakan ta biyo bayan hukuncin kotu na farkon watan Oktoba da ya hana Silva tsayawa takara bisa hujjar an rantsar da shi gwamnan Bayelsa sau biyu duk da cewa shekaru 5 ya yi kacal.

Takardar sunayen yan takarar ta ƙarshe da INEC ta Sanya a shafin ta na internet tana dauke ne da sa hannun sakatariyar hukumar ta INEC Rose Oriaran Anthony.
Kwamitin Gwamnatin Kano na tantance ma’aikatan da Ganduje ya dauka aiki ya mika rahotansa
Yayin da aka fitar da jerin sunayen karshe na ‘yan takarar gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, jam’iyyar APC ba za ta shiga zaben jihar Bayelsa ba sai dai idan kotu ta yanke hukunci kafin ranar zaben.
Gurbin sunayen dan takarar jam’iyyar APC da abokin takararsa, an bar shi babu komai bisa “umarnin kotu” .

Oriaran-Anthony, a cikin takardar da aka yi wa kwaskwarima, ya bayyana cewa matakin da hukumar ta dauka na yin biyayya ga umarnin kotu ne yasa ta cire sunan dan takarar APC.